Dan Najeriya ya kafa sabon tarihi a gasar tsere ta yankin Asiya
Wani dan Najeriya mai kimanin shekara 24 Femi Ogunode ya zama zakara a gasar tsere ta yankin Asiya. Kamar yadda kafar sadarwa ta Premium Times ta kalato, dan tseren wanda aka haifa a garin Akoko da ke Jihar Ondon Najeriya ya samu nasarar kafa sabon tarihi ne a gasar da ake wa lakabi da Asian […]

Wani dan Najeriya mai kimanin shekara 24 Femi Ogunode ya zama zakara a gasar tsere ta yankin Asiya.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Premium Times ta kalato, dan tseren wanda aka haifa a garin Akoko da ke Jihar Ondon Najeriya ya samu nasarar kafa sabon tarihi ne a gasar da ake wa lakabi da Asian Athletics Championsships a ranar Asabar da ta wuce a tseren mita 100 inda ya zama na farko a minti 9 da sakan 1. Wannan nasarar da ya samu ta sa ya doke tarihin da ya taba kafawa da kansa na minti 9 da sakan 93.
A lokacin da yake hira da ’yan jarida, Ogunode ya bayyana cewa “Idan Allah Ya ba ka ni’ima sai ka gode maSa don haka wannan nasara da na samu ni’ima ce daga Allah, kuma ina mika godiyata a gareShi”.
Ina murnar lashe lambar zinare ne da na yi a gasar da hakan ta sa na zama zakara a yankin Asiya.
Ogunode wanda ya taba yin wasan damben boding daga baya ne ya koma na kwallon kafa, daga baya a shekarar 2006 ce ya koma yin tsere. A wata tattaunawa da wata jaridar watsa labarin wasanni a katar ta yi da shi ya bayyana dalilin da ya sa ya bar Najeriya ya koma katar don cigaba da fafatawa a tsere. Ya ce ya yanke hukuncin barin yi wa Najeriya gudu ne bayan an wulatankashi ana gab da tafiya wata gasar tsere a Afirka. Ya ce ana gab da tafifa gasar ce sai jami’an da ke horar da su suka cire sunansa daga jerin ’yan tseren da za su wakilci Najeriya ba tare da wani kwakwaran hujja ba. Hakan ta sa ya yi fushi kuma ya yanke shawarar barin kasar inda ta koma katar.
Ya ce ga shi yau Allah Ya yi hukuncinsa inda ya zama zakara a daukacin Nahiyar Afirka a matsayin wanda ya fi kowane dan tsere kwazo da nuna bajinta. “Ban yi nadamar barin Najeriya kuma na koma katar ba, kuma ina fata wannan ya zama darasi ga Najeriya a kan masu wakiltarta a wasanni daban-daban”, inji shi.
Ya ce da farko ya dauko kasada ne a lokacin da ya bar Najeriya amma daga baya sai ya gwammace gwanda ma da ya bar Najeriya inda yanzu ya cimma burinsa na zama zakara.