Dan Najeriya ya mutu a lokacin da yake kwallo a Turai
Wani dan Najeriya dan kimanin shekara 16 mai suna Shetemi Ayetigbo ya mutu a lokacin da yake kwallo a kasar Ireland a ranar Lahadin da ta gabata. Marigayin, wanda yake buga wa kulob din ’yan kasa da shekara 16 mai suna Belbedere Football Club da ke Dublin na Ireland a matsayin dan kwallon tsakiyar fili […]
Wani dan Najeriya dan kimanin shekara 16 mai suna Shetemi Ayetigbo ya mutu a lokacin da yake kwallo a kasar Ireland a ranar Lahadin da ta gabata.
Marigayin, wanda yake buga wa kulob din ’yan kasa da shekara 16 mai suna Belbedere Football Club da ke Dublin na Ireland a matsayin dan kwallon tsakiyar fili watau (Midfielder) ya mutu ne ba tare da sun yi arangama ko ya bugu da wani abu a cikin filin ba.
Kafar sadarwar Daily Mirror ta kalato cewa ana cikin yin kwallo a tsakanin kulob dinsa da na St Kebins’s Boys ne, kuma shafe kimanin mintuna 25 zuwa 30 ana wasa, sai kawai aka ga ya yanke jiki ya fadi.
Wani da al’amarin ya faru a kan idonsa ya shaida wa kafar sadarwar cewa “Babu wani arangama da dan kwallon ya yi da wani, mun hango shi yana tsaye ne a gefe sai kawai muka ga ya yanke jjiki ya fadi. Takwarorinsa da ke filin ne suka kai masa daukin gaggawa inda suka rika kururuwar da ta ja hankalin jami’an da ke kula da yadda wasan ke gudana kuma aka garzaya da shi asibiti mafi kusa amma kafin a isa ya cika”.
Daga nan ne hukumar shirya wasan kwallo a yankin ta dage wasan zuwa wani lokaci. Sai dai ’yan kwallon da daukadin magoya bayansu sun kadcu matuka da wannan al’amari.
A lokacin da al’amarin ya faru babu ’yan kallo da yawa a filin don wasa ne na karshe a kakar wasa ta bana a gasar rukuni-rukuni ajin ’yan dagaji.
Idan za a tuna a makon jiya Aminiya ta kawo labarin wani da ya mutu a lokacin da yake kwallo a Ajantina don haka al’amarinmutuwar ’yan kwallo a filin wasa ba sabon abu ba ne.