Dan Najeriya ya saya wa karensa motar Naira miliyan biyu

Ina son karena kamar dana, kuma ina son bikin ranar haihuwarsa ya zama na musamman.

Dan Najeriya ya saya wa karensa motar Naira miliyan biyu

Wani kare a cikin mota

Masu iya magana sun ce kowa ya dade zai ga dadau, wani dan Najeriya mai suna Doktor Skidon ya shirya gagarumin bikin don murnar ranar haihuwar karensa tare da saya wa karen motar Naira miliyan biyu.

An gudanar da gagarumin bikin wanda ya samu halartar abokai da masoya a gidansa.

A wani bidiyo da aka sa a shafukan sada zumunta an ga Doktor Skidon da abokansa suna sanya suturar shat kafin su fara yi masa ruwan kudi.

An yanka kek a yayin bikin inda daga nan Doktor Skidon ya raba alawa tare da taimakon abokinsa.

A cikin bidiyon an ji Doktor Skidon yana bayyana karen da dansa don haka ne ya zabi sayen motar da sunan karen.

“Ina son karena kamar dana, kuma ina son bikin ranar haihuwarsa ya zama na musamman.

“Ya cancanci a kyautata masa, kuma ina son in nuna masa yadda nake kula da shi,” in ji Doktor Skidon.

Gagarumin bikin ya samu bayyana ra’ayoyi mabambanta a shafukan sadarwar zamani, inda wasu suka caccaki abin da Doktor Skidon ya yi, yayin da wasu suka yaba masa kan nuna wa karensa kauna.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta