Dan Najeriya ya tsaya takarar Gwamna a Amurka
Wani dan Najeriya mai shekara 34, Austin Chenge, ya shiga takarar Gwamnan Jihar Michigan ta kasar Amurka a zaben da za a gudanar a shekarar 2022. Shugaban Sashen Watsa Labarai da Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abdul-Rahman Balogun, ya bayyana haka a wata takardar da ya fitar. Dan […]
Wani dan Najeriya mai shekara 34, Austin Chenge, ya shiga takarar Gwamnan Jihar Michigan ta kasar Amurka a zaben da za a gudanar a shekarar 2022.
Shugaban Sashen Watsa Labarai da Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abdul-Rahman Balogun, ya bayyana haka a wata takardar da ya fitar.
- Dan Najeriya zai zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya
- Trump ya nada dan Najeriya a matsayin mai ba shi shawara
- Dan Najeriya ya zama Ministan Shari’a a Canada
Balogun ya ce Chenge, wanda dan asalin Jihar Binuwai ne, zai kara da Dan Majalisar Wakilan Amurka Lamar Smith, a karkashin tutar jam’iyyar Republican.
Chenge ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Michigan ne a watan Maris, 2020, wanda hakan ya sa ya zama dan jam’iyyar Republican na farko da ya taba yin haka.
Ya kuma wasa Chenge da cewar baiwa ne ga kasar Amurka saboda kwazon da yake da shi na aiwatar da abubuwan da ake tunanin ba za su yiwu ba.
“Chenge ya kammala karatunsa na Lauya a Jami’ar Birmingham ta kasar Ingila kuma tun a shekarar 2018 yake aiki da Hukumar Sojin Amurka.
“An ba shi lambar yabo ta musamman a matsayin wanda ya kammala karatunsa da jimillar maki (CGPA) 99.8% da kuma kwazo lokacin ganiyar aikinsa”, inji sanarwar.
Ya ce Chenge ya yi suna a Najeriya lokacin da ya yi babur mai kafa uku, wanda ya sanyawa suna ‘Wazobia Tricycle’, a shekarar 2026.
A lokacin, Chenge ya ce ya kirkiri babur din ne domin ya kawo sauki ga rayuwar manoma a Afirka baki daya.