Dan Najeriya ya warware matsalar lissafin shekara 156
Wani malamin jami’a a Najeriya Dokta Opeyemi Enoch, ya warware matsalar lissafin Riemann Hypothesis da aka yi takaddamar warware matsalar cikin shekaru 156.Dokta Opeyemi Enoch, malami ne da ke koyar da darussan lissafi a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Oye a Jihar Ekiti, ana kuma sa ran ya samu kyautar Dala miliyan daya, wato daidai […]
Wani malamin jami’a a Najeriya Dokta Opeyemi Enoch, ya warware matsalar lissafin Riemann Hypothesis da aka yi takaddamar warware matsalar cikin shekaru 156.
Dokta Opeyemi Enoch, malami ne da ke koyar da darussan lissafi a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Oye a Jihar Ekiti, ana kuma sa ran ya samu kyautar Dala miliyan daya, wato daidai da Naira miliyan 200.
Ita kuwa kafar sadarwar Canbas cewa ta yi malamin ya yi ikrarin warware matsalar ta kafar (nehttp://canbas.scoopwhoop.com/article/nigerian-professor-claims-to-habe-solbed-a-century-old-math-problem), Kafafen yada labaran da suka bayyana labarin wannan malami amsanin lissafi dan Najereiya, sun hada da BBC Landan sashen Hausa da jaridar ThisDay ta ranar Litinin 17 ga watan Nuwambar bana.
Malamin, wanda haifaffen Jihar Kogi ne yayio aikin bincike kan yadda za a samar da wutar lantarki daga tartsatsin tsawa, sannan ya yi nasarar bullo da wani salon lissafi da in aka yi amfani da shi za a samu nasarart kare bututun mai daga mabarnata. Kuma a halin yanzu yana aiki a kan dumamar yanayi.