Dan Najeriya ya zama Ministan Shari’a a Canada

Kaycee Madu shi ne bakar fata na farko da ya zama Ministan Shari’ar

Dan Najeriya ya zama Ministan Shari’a a Canada

Kaycee Madu, Ministan Shari’a a Kanada

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Kaycee Madu haifaffen Najeriya murnar nada shi a matsayin Ministan Shari’a Babban Mai Gabatar ta Kara Gwamnatin Alberta, a kasar Canada.

Sanarwa a ranar Alhamis ta hannun mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ta yi alfahari da Madu tarihi da ya kafa na zama ministan sharia’a bakar fata na farko a Canada.

Shugaban, wanda ya bayyana matsayin a matsayin “babban abun tarihi”.

Ya kara da kira ga ‘yan Najeriya a gida da wadanda ke zaune a wasu kasashe da su zama jakadu nagari.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram