Dan Najeriya zai zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya

Dan Najeriya, Farfesa Tijjani Mohammed Bande ya zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya, inda zai maye gurbin Maria Fermanda Espinosa Garces. Maria Fermanda Espinosa Garces ce ta bayyana hakan a lokacin da ta kawo ziyara a Fadar Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja. Shi dai Farfesa Bande shi ne wakilin Najeriya na dindindin a […]

Dan Najeriya zai zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya

Dan Najeriya, Farfesa Tijjani Mohammed Bande ya zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya, inda zai maye gurbin Maria Fermanda Espinosa Garces.

Maria Fermanda Espinosa Garces ce ta bayyana hakan a lokacin da ta kawo ziyara a Fadar Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja.

Shi dai Farfesa Bande shi ne wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya kafin a zabe shi a matsayin wanda zai jagoranci zaman majalisar.

Farfesa Bande haifaffen  garin Zagga ne da ke Jihar Kebbi, kuma ya taba zama shugaban Makarantar Horar da Manayan Ma’aikata wato NIPPS, da ke Kuru a Jihar Filato, sannan kuma tsohon Shugaban Jami’ar Usman Danfodio ne da ke Sakkwato.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara