dan okada ya nemi kashe kansa saboda jabun takardu

A ranar Alhamis ta makon jiya wani dan okada ya yi tsalle ya kubce daga hannun jami’an binciken takardun abubuwa hawa ya kwanta a kan babban titin Ring Road da ke Ibadan, yana jiran motoci su markade shi. An gano cewa, mutumin, wanda ba a gane sunansa ba, ya yi kokarin hallaka kansa ne a […]

dan okada ya nemi kashe kansa saboda jabun takardu

A ranar Alhamis ta makon jiya wani dan okada ya yi tsalle ya kubce daga hannun jami’an binciken takardun abubuwa hawa ya kwanta a kan babban titin Ring Road da ke Ibadan, yana jiran motoci su markade shi.
An gano cewa, mutumin, wanda ba a gane sunansa ba, ya yi kokarin hallaka kansa ne a dalilin gano takardun bogi da yake tare da su a lokacin da jami’an binciken abubuwan hawa suka tsayar da shi domin nuna musu takardun mallaka da iznin yin okada, kamar yadda gwamnatin jihar ta nemi dukkan masu haya da babur su biya Naira dubu 3 shaidar rajista.
Wata majiya da al’amarin ya auku a kan idanunta, ta shaida wa wakilinmu cewa, a daidai lokacin da jami’an suka nemi wannan mutumi ya nuna musu takardun mallaka da iznin hukuma, sai ya zaro su daga cikin aljihunsa ya mika musu, sai dai bayan binciken nasu suka tabbatar masa cewa, jabun takardu ne, amma ya dage a kan takardun nasa na kwarai ne. Sai dai a yayin da ya fahimci jami’an da gaske suke yi, sai kawai ya yi wuf ya fada kan titi a kusa a karkashin wata tirela yana so ta kashe shi ya huta. Ya sake kwantawa a karkashin wata karamar mota da yake so rayuwar tasa ta kare ta wannan hanya, amma jami’an da suke yin binciken, tare da taimakon wasu mutane sun hanzarta kai masa dauki, musamman da yake a hankali motoci suke tafiya a wannan lokaci da ake yin binciken, suka kawar da shi zuwa bakin hanya.
Bayan an ceto shi, mutumin ya some, ya yi ta fitar da wani ruwa daga bakinsa, wanda ya haifar da ’yan sanda suka garzaya da shi asibitin gwamnati na Adeoyo. Har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba mu ji duriyar irin halin da wannan mutumi yake ciki ba.