dan Osama ya yi barazanar daukar fansar kashe mahaifinsa

dan marigayi jagoran kungiyar Alka’ida, Osama bin Laden, mai suna Hamza bin Laden ya yi barazanar daukar fansa a kan Amurka kan kashe mahaifinsa.Wani sakon murya mai tsawon mintin 21 mai taken “Dukkan Osamomi ne,” da aka sanya a kafar labarai ta SITE Interlligence Group ta intanet, ya ruwaito Hamza bin Laden yana alkawarin ci […]

dan Osama ya yi barazanar daukar fansar kashe mahaifinsa
dan Osama ya yi barazanar daukar fansar kashe mahaifinsa

dan marigayi jagoran kungiyar Alka’ida, Osama bin Laden, mai suna Hamza bin Laden ya yi barazanar daukar fansa a kan Amurka kan kashe mahaifinsa.
Wani sakon murya mai tsawon mintin 21 mai taken “Dukkan Osamomi ne,” da aka sanya a kafar labarai ta SITE Interlligence Group ta intanet, ya ruwaito Hamza bin Laden yana alkawarin ci gaba da amfani da makamai da kungiyar ke yi a kan Amurka da kawayenta
 “Za mu ci gaba da kai muku hare-hare mu tunkare ku da hare-hare kuma mu tunkare ku a kasarku da kasashen waje don mayar da martani kan zaluncinku a kan mutanen Falasdinu da Afghanistan da Syria da Iraki da Yemen da Somaliya da sauran kasashen Musulmi da ba su tsira daga zaluncinku ba,” inji Hamza bin Laden.
Ya kara da cewa: “daukar fansar kasar Musulunci ga Sheikh Osama Allah Ya yi  masa rahama ba daukar fansa ce ga Osama a kashin kansa ba, a’a daukar fansa ce ga dukkan wadanda suka kare martabar Musulunci.”
Sojojin Amurka sun kashe Osama bin Laden a kasar Pakistan a shekarar 2011, kuma wasu takardu da Amurka ta samu a gidan Bin Laden kuma aka buga su a bara, sun yi zargin cewa mukarrabansa sun yi kokarin hada Osama da dansa Hamza wanda ake yi masa daurin talala a wani gida a kasar Iran.
Hamza mai shekara 20 zuwa sama ya kasance tare da mahaifinsa a Afghanistan kafin harin 11 ga Satumba, kuma ya dauki lokaci tare da shi a Pakistan bayan Amurka ta mamayi kasar Iraki.