Dan Ronaldinho Joao Mendes ya kulla yarjejeniya da Barcelona 

Mendes mai shekaru 18 ana ganin zai bi sahun mahaifinsa.

Dan Ronaldinho Joao Mendes ya kulla yarjejeniya da Barcelona 

Dan tsohon tsauraron Barcelona Ronaldinho wato Joao Mendes ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

A yanzu Mendes wanda saurayi ne zai faro daga matakin ’yan wasa ’yan kasa da shekaru 19 yayin da kuma zai samu horo a kwalejin horar da matasan ’yan wasan kungiyar.

Mendes mai shekaru 18 ana ganin zai bi sahun mahaifinsa ne wanda ya shafe shekaru 5 yana taka leda da Barca.

Dan wasan wanda a baya ke taka leda da kungiyar kwallon kafa ta Cruzeiro wadda ke doka gasar Serie B ta Brazil, ya kawo karshen kwantaragin nasa ne bayan samun damar taka leda da kungiyar ta Barcelona don bin sahun mahaifinsa.

Rahotanni sun ce Mendes bai yi amfani da sunan mahaifinsa wajen samun kwantaragin da Barcelona ba.

Haka zalika ba da sunan mahaifinsa ya samu damar taka leda da Cruzeiro ba, hasalima sai bayan tabbatuwar samun shiga kungiyar tukunna da dama suka san waye mahaifin nasa.

Ronaldinho mai shekaru 42, tun bayan ritaya daga fagen tamaula, yanzu haka yana matsayin jakadan Barcelona ne.

Kwantaragin na Mendes na nuna cewa matashin dan wasan zai samu horo a fitacciyar kwalejin La Masia wadda ta yaye ’yan wasa irinsu Lionel Messi da Gerard Pique da kuma Xavi Hernandez.