Dan sakandare ya yanke wuyan karamin yaro da reza a Maiduguri
Ya kira dan karamin ajin ne da tsakar dare zuwa wurin da babu kowa yayyanke jijiyon wuyansa
Wani dalibin sakandare da ya yi yunkurin kashe wani dan karamin aji ta hanyar yanke masa jiyoyin wuya da reza a makaranta ya shiga hannu.
Wanda ya yi aika-aikan dai dalibin aji biyu ne na Babbar Sakandare kuma a halin yanzu yana hannun ’yan sanda masu binciken manyan laifuka a Maiduguri, Jihar Borno.
- ‘Na dauki ci da sayar da sassan jikin mutane a matsayin al’ada’
- Zan bar Najeriya fiye da yadda na karbe ta —Buhari
Majiyar Aminiya ta shaida mata cewa abin ya faru ne a shahararriyar makarantar nan ta El-Kanmi College of Islamic Theology da ke Maiduguri, a bayan wani dakin kwanan dalibai da dare.
Majiyar ta ce dalibin da aka kashe, bai wuce shekara 12 a duniya ba, ya gamu da ajalinsa ne bayan wani dan aji biyu a Babbar Sakandare ya aike shi, shi kuma ya ki zuwa aiken.
Daga baya sai wanda ya aike shin ya kira shi da tsakar dare zuwa wani wuri da babu kowa, ya sanya reza ya yanke shi a tsakiyar wuyansa, ya kuma yayyanke jijiyoyin wuyan.
Washegari ne aka tsinci karamin yaron a kwance jina-jina, rai kwawai, mutu kwakwai, a bayan dakin kwanan.
Nan take aka wuce da yaron zuwa Bangaren Gaggawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda a halin yanzu ake ba shi kulawa domin ceto rayuwarsa.
Majiyar ta ce a halin yanzu dai karamin yaron yana can a kwance, rai kwakwai, mutu kwakwai.
Wani malami a makarantar ya ce bayan haka ne hukumar makarantar ta kira ’yan sanda suka tsare tare da yin awon gaba da wanda ake zargin zuwa Bangaren Binciken Laifukan Kisa da ke karkashin Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno.
Wani malamin makarantar da ya bukaci Aminiya ta sakaya sunansa ya yi zargin yawan rashin tsawatarwa da kuma ladabatar da dalibai, yawanci saboda abin duniya da malaman suke samu daga hannun iyayen yaran.
Malamin ya bayyana takaicinsa game da abin da ya faru, da kuma abin da ya kira halayyar wasu malaman makarantar ga daliban kwana, wadanda yawancinsu ’ya’yan manyan mutane ne.