Dan sanda mafi tsawo a duniya
Jagdeep Singh daga kasar Indiya shi ne dan sandan da aka ce ya fi kowa ne dan sanda tsawo a duniya, inda ya kasance da tsayin kafafu da hannuwa da hakan ya sa duk mai sha’awar daukar hoto da shi sai dai ya yi amfani da tsani. Singh mai tawon kafa 7 da inci 6, […]
Jagdeep Singh daga kasar Indiya shi ne dan sandan da aka ce ya fi kowa ne dan sanda tsawo a duniya, inda ya kasance da tsayin kafafu da hannuwa da hakan ya sa duk mai sha’awar daukar hoto da shi sai dai ya yi amfani da tsani.
Singh mai tawon kafa 7 da inci 6, yana kokarin kiyaye dokokin da aka tanada a Punjab wajen da yake aiki inda ya kasance babu wani dan sanda da ya kai koda kafadarsa ce a tsayi haka ma sauran jama’ar gari. dan sandan yana aiki ne a yankunan da yake don hana abubuwa da za su iya kawo matsala ga al’umma. Tsawo da girman jikin Singh ya sa ya ware telan da ke dinka masa kakinsa yayin da ake yi masa odar takalmi daidai kafarsa daga kasashen waje wanda ya kai lambar takalmi 19. A shekarun baya dai an sanar da cewa, Rajesh Kumar daga garin Haryana ta kasar Indiya ne ya fi kowane dan sanda tsawo a duniya inda yake da tsawon kafa 7 da inci 4, hakan ya sa a yanzu ya zama na biyu a bayan Singh. Singh ya kai shekara 20 yana aiki da hukumar ’yan sandan Indiya yana kuma alfahari da aikin da yake yi inda yake cewa, “Ina alfahari da cewa, ni ne dan sandan kasar Indiya mafi tsawo a duniya, ina da tsawon kafa 7 da inci 6, sannan ina da karfin daga nauyin da ya kai kilo 190, ina murna da hakan.” A yayin da Singh yake alfahari da kasancewarsa mafi tsawo a tsakanin ’yan sandan duniya sai dai kuma yana fuskantar wasu matsalolin rayuwa. Ya bayyana matsalolin da cewa, “Ina fuskantar matsalolin da suka hada da ba zan iya sayen kayan sawa da ya yi daidai da jikina ba, ba zan iya amfani da ban-daki kamar kowa ba, ba zan iya tafiya a cikin motar haya ba, sai dai in yi amfani da motata saboda duk sun yi min kankanta.”
Singh ya ci gaba da cewa, “Ina fuskantar matsala ta bangaren soyayya, ban samu mace mai tsawona da za mu dace ba, kuma ba wacce take da shirin ta aure ni saboda jama’a da dama na yi min kallon tsawona ya yi yawa. Sai dai akwai wata mace mai suna Sukhbir Kaur mai tsawon kafa 5 da inci 11 duk da haka ta yi masa gajarta. Duk da shaharar da Singh ya yi a Punjab tsawonsa ya janyo masa suka a kafofin shafukan sada zumunta. Mutumin da ya fi kowa tsawo a duniya shi ne Sultan Kösen, mai kafa 8 da inci 2.8 daga garin Ankara ta kasar Turkiyya da aka gano a ranar 8 Faburairun 2011.