Dan sanda mutum-mutumi zai rika aikin tsaro a Dubai
Masarautar Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa ta samar da dan sandan mutumutumi mai motsi na Robocop da zai karade birnin kamar sauran jami’an hukuma, inda a halin yanzu ya fara aiki a manyan shagunan sayar da kayayyakin masarufi da titunan birnin. Kuma nan da shekarar 2030 Masarautar Dubai za ta tabbatar da cewa kashi […]
Masarautar Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa ta samar da dan sandan mutumutumi mai motsi na Robocop da zai karade birnin kamar sauran jami’an hukuma, inda a halin yanzu ya fara aiki a manyan shagunan sayar da kayayyakin masarufi da titunan birnin. Kuma nan da shekarar 2030 Masarautar Dubai za ta tabbatar da cewa kashi 30 cikin 100 na ’yan sandanta duk mutum-mutmi ne mai motsi da zai rika taimaka wa al’umma a harkokin tsaro. Don haka idan kana son kai rahoton miyagun laifukan da aka aikata, sai ka yi kiran neman taimako, ko ka yi amfani da kafar sadarwa a shafinsu na intanet, nan take dan sandan Robocop zai amsa maka.
Wannan dan sanda yana da tsawon sentimita 170 da nauyin kilo 100, kuma zai rika gudanar da ayyukansa a manyan shagunan sayar da kayan masarufi da tituna, sannan zai rika taimaka wa mazaunan birnin da masu yawon bude ido.
An baje samfurin dan sandan Robocop da malamin makaranta mai motsi da fasahar magana da kurame ba bebeye, in su shiga matsala ga yadda za su tuntubi ’yan sanda a wajen bikiun baje kolin fasahar kere-kere na zamani da aka yi mako gudana ana gudfanarwa a Dubai. Kamfani kere-kere na Gited ne ya gudanar da shirin.
Sashen tarairayar fasahar kere-keren zamani na’yan sandan Dubai zai gabatar shiri tare da baje hotunan bidiyon yadda mutane za su hulda da sabon dan sandan, inda za a nuna yadda za a latsa maballin neman taimako (SOS button), wan da muytane za su latsa in sun shiga matsanancin halin neman taimako.
“Idan mutum ya latsa maballin , to ya ankarar da su cewa suna neman daukin gaigawa, ta yadda da sun ci gaba sai jami’in ’yan sanda ya iso wajensu cikin minti biyar,” a cewar Major Ahmed Al Haj, shugaban sashen kasuwancin zamani na a rundunar ’yan sandan Dubai, kamar yadda ya bayyana wa jaridar Khaleej Times a wajen bikin bajen kolin makon fasahar kere-keren zamani na Gited.
Duk da cewa an fara aiki da dan sandan mutum-mutumin Robot a halin yanzu, to mazaunan birnin su san da cewa, “daruruwansu za su baibaye titunan birni” nan da ’yan shekaru kadan.
“Irin wannan dan sanda dai zuwa yanzu ya fara aiki a katyafaren shagon The Dubai Mall and Mirdif City Centre. Mutane na iya amfani da Robot su biya tara, ko neman izinin ’yan sanda, da sauran hada-hadar intanet, ta hanyar aikewa da sakonni tes da magana cikion sauri,” inji shi.
Ta hanyar amfani da alamun fasahar tantance fuska, zai iya gano “masu laifin da ake nema.” “da zarar ya gano mutumin da ke cikin jerin mutanen da ake nema, nan da nan zai ankarar da dakin sadarwar, in da jami’ai za su fito cikin shiri,” inji Al Haj.
An damfare shi da na’urorin sarrafawa don mu’amala da mutane, ta yadda za ka iya ganin Robot yana sara wa masu amfani da shi, yana kuma tambayar ko kun kwana lafiya. Don haka kaddamar da dan sandan Robocop na farko a duniya bude sabon babi ne da ke share wa Dubai fagen zama ja-gaba a biranen duniya da ke amfani da fasahar kere-kere. Wani kamfani na kasar Denmark mai suna Komas ya baje kolin Farfesan ilimi na Robot (Soren Ramussen). Sannan an samar da na’urar safar hannu guda da ke fassara wa ’yan sanda kalaman bebaye ko kurame ko duk wani da ked a matsalar jin Magana. Na’urar dai an ce tana fassara haruffa 26 da ake amfani das u wajen harhada kalmomi.