Dan sanda ya bindige abokin aikinsa a lokacin da ya tarwatsa ‘Yan acaba
Wani jami’in dan sanda da ke bakin aiki a yankin Igando a Jihar Legas ya gamu da ajalinsa bayan da abokin aikinsa ya harbe shi da bindiga bisa kuskure a lokacin da yake kokarin tarwatsa gungun masu baburan acaba da babur mai kafa uku da suka yi cuncurundo suna neman hana jami’an ‘yan sandan yin […]
Wani jami’in dan sanda da ke bakin aiki a yankin Igando a Jihar Legas ya gamu da ajalinsa bayan da abokin aikinsa ya harbe shi da bindiga bisa kuskure a lokacin da yake kokarin tarwatsa gungun masu baburan acaba da babur mai kafa uku da suka yi cuncurundo suna neman hana jami’an ‘yan sandan yin aikinsu.
Bincikin da Aminiya tayi ya nuna cewa, an tura ‘yan sandan yankin Igando ne a jihar Legas domin suyi maganin cunkoson ababen hawa a yankin, lamarin da ya sanya su yin fito na fito da masu tukin babur na acaba da babur mai kafa uku wadanda ke yin aron hannu guda wato masu bin one way lamarin da ya sanya ‘yan sandan kame masu baburan da dama ganin haka ne yasa suka yi taruwa dango a yankin suna jifan ‘yan sandan da duwatsu abin da ya sanya ‘yan sandan yin harbi a iska domin tarwatsu wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar dan sandan kwantar da tarzoma daya ya kuma jikkata wasu masu baburan acaba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan a Legas DSP Bala Elkana ya tabbatar da faruwar lamarin. ya ce wasu ‘yan acaba biyu ‘yan kungiyar Yarbawa zalla ta OPC ne suka tayar da tarzoma suna kokarin hana ‘yan sandan yin aikin su, ” suna ja’in ja da ‘yan sandan ne har suka dana kunamar bindigar daya daga cikin ‘yan sandan wanda hakan ya sanya harsashi ya fita ya sami daya daga cikin ‘yan sandan kwantar da tarzomar”
Ya ce, ‘yan sandan na kan aikinsu ne na hana ‘yan acabar bin hanyoyin da aka haramta masu.
Wannan lamari dai za a iya cewa, yana da alaka da yawan cunkoson ababenhawa da ke addabar birnin na Legas lamarin da a baya bayan nan ya yi kamari har ya kai ga hukumar ‘yan sandan daukar matakin tura jami’anta dubu guda kan titunan Legas domin magance cunkoson ababan hawan.