dan sanda ya bude wa motar Sarkin Zango wuta
daya daga cikin ’yan sandan da ke sintiri a manyan titunan jihar Jihar Edo ya yi wa motar da Alhaji Muhammadu Jingudo Sarkin Zangon Benin yake ciki ruwan harsasai a ranar Lahadin da ta gabata, a hanyarsa ta dawowa daga wajen daurin aure na dan abokinsa da aka yi a Ijebu-Ode ta Jihar Ogun. Al’amarin […]
daya daga cikin ’yan sandan da ke sintiri a manyan titunan jihar Jihar Edo ya yi wa motar da Alhaji Muhammadu Jingudo Sarkin Zangon Benin yake ciki ruwan harsasai a ranar Lahadin da ta gabata, a hanyarsa ta dawowa daga wajen daurin aure na dan abokinsa da aka yi a Ijebu-Ode ta Jihar Ogun.
Al’amarin ya auku ne lokacin da suka hau kan wani hawa a wani gangare kafin a iso kauyen Ahor mai tazarar kilomita 10 daga Birnin Benin hedikwatar Jihar Edo.
Kuma a lokacin daidai misalin karfe shida saura kwata na yamma lamarin ya faru. Kuma Sarkin Zango, Alhaji Muhammadu Jingudo yana a gaban motar, tare da Sarkin Fulani Benin Ardo Alhaji Muhammadu Usman da mukarrabansu, tare da wani dan sanda mai mukamin sufeto, mai suna Iliya Musa mai aiki a hedikwatar hukumar ’yan sanda ta jihar
A cikin wannan mota akwai wakilin Aminiya da Shugaban ‘yan Banga na Benin, Alhaji Shuaibu Muhammed KT tare da abokan Angon.
Wannan dan sandan da ya bude wa motar wuta daga nesa da ya ga direban ya doshi wannan gangaren kawai kafin a ce kwabo ya bar abokan aikinsa suna tsaye a gefen hanya, sai ya zabura ya je ya hau kan hanya ya tsaya a tsakiyar kwalta, ganin haka sai direban ya yi kokarin kauce masa domin kada ya taka shi, kafin wani lokaci kawai wannan dan sanda sai ya fara harbin motar babu kakkautawa.
Wannan barin wuta ya tsoratar da Auwalu direba, domin harbin ya yi yawa sai ya kara taka motar ya yi gaba.
Kuma wannan sufeton dan sandan da ke cikin motar tare da Sarkin Zango abin ya harzuka shi matuka, ganin ‘yan uwansa ne suka yi wannan aika-aikar, don haka nan take ya dauki wayarsa ya kira Mista Basi, wanda yake shi ne Shugaban sashin wadannan ’yan sandan sintiri a manyan titunan kasar nan ya shaida masa abin da ya faru, amma Mista Basi din ya ki ya daukar wayar, a karshe dai sai ya kulle wayarsa gaba daya.
Irin wannan ya taba ya faruwa a wani lokaci can baya, inda dan sanda ya nemi wani direba ya ba shi Naira 20 na goro kafin wannan direban ya tsaya ya samu ya gyara fakin, kawai sai ya ji karar bindiga tau! dan sandan ya harbe masa yaron mota, Kuma da suka tabbatar sun aikata katobarar a lokacin ba su tsaya sun jira ba suka ranta a na kare.
Al’amura irin wadannan na ci gaba da faruwa a kan hanyoyin kasar nan idan suka aikata barnar ba su tsayawa a same su, sai su dauki motarsu su bar wurin su yi gaba.