Dan sanda ya harbe abokin aikinsa har lahira a Kano

Dan sandan ya ce ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ya yi harbin.

Dan sanda ya harbe abokin aikinsa har lahira a Kano

Wani hafsan dan sanda ya harbe abokin aikinsa, Sajan Bashari  Alhassan, har lahira, bayan wani rikici da ya barke a tsakaninsu a Jihar Kano.

Al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a wani ofishin ’yan sanda da ke Karamar Hukumar Warawa ta jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “An samu rashin jituwa tsakanin jami’an biyu, a dalilin haka ne Sufeton ya harbi shi Sajan din.

“Bayan gudanar da bincike, Sufeton ya yi ikirarin cewa bai ma san ya harbi abokin aikin nasa ba, abin da kawai zai iya tunawa shi ne Sajan din na yi masa dariya. Don haka ya fita daga hayyacinsa kuma ya aikata wannan danyen aiki”.

Kiyawa ya ce an garzaya da wanda aka harba din zuwa Babban Asibitin garin Wudil, inda a can likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Ya kara da cewa an tsare Sufeton da ya yi harbin nan take, an kuma mika shi ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) domin gudanar da bincike a kan lamarin, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar.

Ya ce kuma ce an ba da umarnin a kai wanda ake zargin zuwa asibiti domin a bincika lafiyarsa.