Ɗan sanda ya harbe mace mai shayarwa har lahira

Wata mata mai shayarwa ta rasu bayan da wani ɗan sanda ya ɗirka mata harbi a bakin titi.

Ɗan sanda ya harbe mace mai shayarwa har lahira

Gawa

Wata mata mai shayarwa ta rasu bayan da wani ɗan sanda ya ɗirka mata harbi a bakin titi.

Ɗan sandan ya harbe matar be a bisa kuskure a lokacin da ya buɗe wuta a ofishin ’yan sanda na Oke Ila a garin Ado Ekiti, fadar Jihar Ekiti.

Dan sandan ya kai ziyara ofishin ne daga wata Shiyya domin taya abokam aikinsa murnar samun ƙarin girma.

A garin haka ne ya yi harb, wanda harsashi ya sami matar da ke gefe hanya daga tsallaken titi.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, wanda aka yi wa karin girma a kwanan nan, AIG Adeniran ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kwace bibdigar dan sandan kuma a halin yanzu yana tsare ana gudanar da bincike