Dan sanda ya harbe mahaifinsa har lahira a Borno

Mahaifin nasa da ya hallaka tsohon dan sanda ne mai muƙamin ASP

Dan sanda ya harbe mahaifinsa har lahira a Borno

Jami’an ‘Yan sanda

Wani dan sanda mai muƙamin Sajan ya shiga hannu kan zargin  harbe mahaifinsa har lahira a garin Maiduguri na Jihar Borno.

Majiyarmu ta tsaro a jihar ta ce Sajan Sunday Linus Wadzani ya harbe mahaifin nasa ne sakamakon sabanin da suka samu.

“Lamarin ta faru ne da misalin karfe 4.30 na yamma ranar Lahadi, 21 fa watan Yuli, 2024,” a cewar majiyar tamu.

Aminiya ta samu rahoto cewa mahaifin da sandan da ya bindige tsohon dan sanda ne mai muƙamin ASP.

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Modugannari da ke kusa da hedikwatar ’yan sanda ta jihar.

Majiyarmu ta ce Sajan din da ke aiki a Majalisar Dokokin Jihar Borno ya shiga hannu, inda ake tsare da shi a ofishin ’yan sanda na unguwar GRA.

Kokarin wakilinmu na samun karin bayani kan lamarin bai yi nasara ba, zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.