Dan sanda ya harbi jarumin Nollywood

’Yan sanda sun tabbatar da harbin da wani jami’insu ya yi wa jarumi kuma daraktan fina-finan Nollywood a wurin casu

Dan sanda ya harbi jarumin Nollywood

Dan sandan Najeriya (Tsohuwar ajiya).

Hukumar ’yan sanda ta tabbatar da labarin harbin da wani jami’inta ya yi wa fitaccen jarumi kuma daraktan fina-finan Nollywood, Azeez Ololade Ijaduade, a wurin casu a Jihar Ogun.

Labarin harbin harbin ya bazu a shafukan sada zumunta ne a daren Asabar bayan da abokin aikin jarumin, Abiodun Adebanjo ya wallafa Instagram cewa: “Wani dan sanda Najeriya sun harbe darakta na, Azeez Ijaduade.

“A halin yanzu dan jarumin yana cikin mawuyacin hali a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Babcock; Duk wanda ke da lambar IG ko kwamishina ya taimaka.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ya bayyana cewa kwanson harsashi ne — ba harsashi ba — ya sami jarumin a wuya.

Ya ce, “A casun karshen shekara na Kamfanin Bramaj a wani otal ne wani dan sandan kwantar da tarzoma ya yi harbi iska, amma abin takaici sai kwanson harsashin ya samu wani jarumi mai suna Azeez Ijaduade a wuya.

“An garzaya da shi asibiti a Ilishan kuma yana samun sauki.”

Odutola ya kara da cewa an kama jami’in da ya yi harbin kuma an fara bincike kan lamarin.

Tinubu zai halarci taron G20 a Brazil

Zaɓen Ondo: Wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu — Tinubu

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku