Dan sanda ya harbi mai kayan marmari a Kebbi
Dan sandan ya dirka wa mutumin harsashi biyu a lokacin da ake dukan wani barawo
Wani dan sanda ya tsallake rijiya a hannun mutane bayan ya harbi wani mai sayar da kayan marmari a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Dan sandan ya harbi Habibu Mohammed, da ke sayar da lemo a kofar Asibitin Sir Yahaya ne a kasan hakarkarinsa ne a lokacin da hatsaniya ta kaure bayan an wani da ake zargi ya saci babur a harabar asibitin.
- Ta hallaka budurwar tsohon saurayinta ta kona gidansa
- Dattijo ya nemi budurwa ta biya shi N50,000 saboda kin auren shi
Wani ganau ya fada wa wakilinmu cewa wasu mutane ne suka kama barawon babur suka kuma mika shi ga jami’an tsaron asibitin.
Ana cikin haka ne jama’a suka far wa wanda ake zargin suka yi awon gaba da shi suna kokarin yi masa dukan kawo wuka.
Ya ce ’yan sanda biyu da ke wurin, daya sanye da kaki dayan kuma a cikin kayan gida, ba su yi wani kokari ba domin kwantar da rikicin.
Ana cikin haka sai dan sandan da ke cikin kayan gida ya karbi bindigar dayan ya harbi Habibu sau biyu.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya ce an kama Kofur Sa’idu Adamu, kuma tuni aka fara bincike a kan lamarin.