Ya harbi surukinsa ya kashe ’yan sanda 6 saboda matarsa

Ya kona jerin wasu gidaje a bariki bayan ya aika ’yan sanda kwantar da tarzoma shida lahira

Ya harbi surukinsa ya kashe ’yan sanda 6 saboda matarsa

Wasu daga cikin jerign gidajen da dan sandan ya kona a cikin bariki. (Hoto: Olatunji Omirin, Maiduguri).

Wani dan sanda ya bude wa surukinsa wuta ya kuma harbe wasu ’yan sandan kwantar da tarzoma shida har lahira kan sabani da iyalinsa.

Bayan bude wutar, dan sandan mai mukamin Sajan, ya kona gidaje da dama, saboda rikicin da yake da matarsa a barikin ’yan sanda da ke Kwalejin ’Yan Sanda a Maiduguri,  Jihar Borno, a daren Alhamis.

Majiyarmu da ke da kusanci da iyalan ta ce, “Ya hahharbi mutane, shida daga cikinsu ’yan sandan kwantar da tarzoma ne kuma sun rasu, wasu biyu kuma ana jinyar su a Asibitin Kwararru.

“Ya harbi surukinsa, sannan ya kona jerin gidaje hudu, kowannensu iyalai takwas ne a ciki.”

Wani makwabcinsa ya ce tun lokacin da ma’auratan suka samu matsala makwabta suka yi ta kokarin sasanta su amma mutumin ya ki.

Wata majiya a barikin ta ce, “Sajan din da matar suna rikici, shi ne ta shaida wa iyayenta cewa yana dukan ta, har ta kwashe kayanta daga gidansa.

“A sanadiyyar kwashe kayan da ta yi saboda yadda ta ce yana musguna mata ne ya bude wa mutane wuta ranar Laraba da dare.”

Wani babban dan sanda a barikin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.

Ya ce, “Suna yawan rikici da matarsa, mu da matan wasu manyan hafsoshinmu mun sha kokarin sasanta su, mun sha yi mishi magana, ba ya ji.”

Ya bayyana cewa bayan matar ta kwashe kayanta ne mijin ya sha alwashin sai ya kashe mutane, idan har ba ta dawo ba.

Ya ce daga baya an yi nasarar tsare dan sandan, bayan da ya yi aika-aikan.

Wata majiyar da ta tsallake rijiya da baya ta shaida wa wakilinmu cewa Sajan din, “Ya zo gidanmu ya fara harbe-harbe, shi ne muka tsere, saboda yana barazanar cewa zai kashe kowa duk a huta.”

Aminiya ta gano cewa a halin yanzu Sajan din yana tsare a Sashen Binciken Manyan Laifuka a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Borno.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga hukumomin ’yan sandan jihar, amma abin ya faskara.