Dan Sanda Ya Kama Masu Ba Shi Cin Hancin N400,000 a Borno
DPO ya kama masu safarar miyagun kwayoyi da suka yi masa tayin cin hancin 400,000 bayan ya kama abokin harkarsu
Wani DPO na ’yan sanda ya kama masu safarar miyagun kwayoyi duk da cewa sun yi masa tayin cin hancin Naira dubu 400 a Borno.
Masu ba da cin hancin sun yi yunkurin ba da cin hanci ne bayan ’yan sanda sun kama wani mai safarar miyagun kwayoyi dauke da buhuna biyu makare da kwayar Tramadol a cikin Keke NAPEP a garin Maiduguri.
Su ukun suna daga cikin mutanen mutane 21 da rundunar ’yan sandan jihar ta kama kan safarar miyagun kwayoyi da kuma ta’ammali da su a sassan Maiduguri.
Daya daga cikin wadanda aka kama ya ya shaida wa manema labarai cewa dubnsa ta cika ne bayan wani binciken kwakwaf da jami’an tsaron da ke sintiri a GRA suka gudanar a mahadar Jiddari.
- Kotu ta dakatar da rushe masarautun Kano
- NAJERIYA A YAU: Abu Na Gaba Da Zai Faru Da Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe
- Ya kamata gwamnati ta sassauta tatsar haraji a wurin ’yan Nijeriya — Sarki Sanusi II
Bayan kama shi, wasu Mutane biyu da ke tare da Abubakar sun tunkari jami’in ’yan sanda na shiyya (DPO) da nufin ba shi cin hancin Naira 400,000 domin a sako wanda aka kama da kwayoyin da yake dauke da su.
Amma DPO, SP Waziri Garba ya ki karbar cin hancin inda ya sa aka kama mutanen nan ta ke.
Tuni dai aka tura su sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike, inda daya daga cikinsu ya tabbatar da kin karbar cin hancin da DPO ya yi.
Wanda ake zargin ya bayyana wa manema labarai cewa: “Mun tuntube shi (DPO) da kudin, amma ya ki, inda ya bayyana cewa magungunan na da illa kuma mun aikata wani babban laifi.
Amma dayan, wanda ya yi ikirarin cewa shi direban Keke Napep ne, ya musanta cewa yana da hannu a safarar miyagun kwayoyi.
A cewar sa shi an umarce shi da ya yi jigilar buhunan ba tare da sanin abin da ke cikinsu ba.
”Ban san abin da ke ciki ba sai da ’yan sanda suka binciki buhunan, nan ne na san da hakan,” in ji shi.
ASP Nahum Kenneth Daso, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Ya jaddada kudirin rundunar na yaki da miyagun ayyuka, ya kuma bukaci mazauna jihar da su kai rahoton duk wani abu da suke damun su zuwa ga lambobin gaggawa kamar haka: 08068075581 da 08023473293 don daukar matakin gaggawa a kai.