Dan sanda ya kashe mutum a garin Aba

Wani dan sanda ya kashe wani magidanci, dan kasuwa mai suna Ikeokwu Onyemachi ranar Larabar da ta gabata, a garin Aba, Jihar Abiya a kokarin da dan sandan yake yi na kwace babur din mamamcin.Lamarin dai ya faru ne a layin Ogbor Hill. Bayanin da Aminiya ta samu, dan sandan yana aiki ne a ofishin […]

Dan sanda ya kashe mutum a garin Aba
Dan sanda ya kashe mutum a garin Aba

Wani dan sanda ya kashe wani magidanci, dan kasuwa mai suna Ikeokwu Onyemachi ranar Larabar da ta gabata, a garin Aba, Jihar Abiya a kokarin da dan sandan yake yi na kwace babur din mamamcin.
Lamarin dai ya faru ne a layin Ogbor Hill. Bayanin da Aminiya ta samu, dan sandan yana aiki ne a ofishin rundunar ’yan sanda ta Eziama.
Mamacin ya gamu da ajalinsa ne yayin da suke kan hanyar sun ta zuwa kauyen Abala, domin rakiyar gawar wani mutum mai suna Pa Okike. Suna tsakar tafiya a babur dinsu suna rakiyar motar gawar mamacin, sun isa kusa da wani karamin ofishin ’yan sanda na Azuka sai wancan dan sanda da ake magana, shi da abokan aikinsa suna cikin wata mota kirar fijo, suka garzayo suka bi su. A kokarin kwatar makullin babur din ne shi kuma mamacin yana kokarin yi masu bayani, aka ce cikin fushi ya fitar da bindiga ya harbe shi.
An gaggauta kai Ikeokwu asibiti, kafin daga bisani rai ya yi halinsa. Wakilin Aminiya ya tuntubi Ezekiel Onyeke, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Abiya game da batun, inda ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya ce Habila Joshak, Kwamishinan ’yan sandan Abiya ya ba da umurnin a kama jami’in a tsare, don haka yana hannu yanzu haka, ana bincike.