Dan sanda ya kashe mutum a kan Naira hamsin

Wani dan sanda ya harbe mutum daya ya mutu, a yayin da ya raunata mutane biyu; a yayin karbar cin hanci, inda direban motar ya ba shi Naira hamsin a hanyar Pariya zuwa Wuru Dole da ke karamar Hukumar Girei, Jihar Adamawa. Al’amarin ya faru ne a sakamakon gardama da ta barke a tsakanin dan […]

Dan sanda ya kashe mutum a kan Naira hamsin

Wani dan sanda ya harbe mutum daya ya mutu, a yayin da ya raunata mutane biyu; a yayin karbar cin hanci, inda direban motar ya ba shi Naira hamsin a hanyar Pariya zuwa Wuru Dole da ke karamar Hukumar Girei, Jihar Adamawa.

Al’amarin ya faru ne a sakamakon gardama da ta barke a tsakanin dan sandan da kuma mutanen da ke cikin motar, kamar yadda shaidun gani da ido da suke wurin suka bayyana kuma suka nemi a sakaya sunansu.

“dan sandan ya bukaci a ba shi cin hanci, sai direban motar ya ce ba zai ba shi fiye da hakan ba. Sai wani mutum da ke dayan gefen motar ya ce da shi ya kamata ya gode don ya samu hamsin domin ba da cin hanci ba ya cikin dokar kasa,” inji su.

Shaidun sun kara da cewa: “Abu kamar wasa sai dan sanda ya dago bindigarsa ya ce zai harbi wanda ya yi magana. Mutumin ya ce ai ba ya tsoron bindiga. Kawai sai muka ji harbi wanda nan take mutumin ya mutu a wajen, sannan harsashen ya taba wadanda ke kusa da mutumin.”

Sun kara da cewa, ganin abin da dan sanda ya yi ya sanya mutanen da ke wajen suka bi shi, suka dasa masa bindigar shi ma suka kashe.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Adamawa, Othman Abubakar ya tabbatar da faruwar al’amarin.