Dan sanda ya kashe sojan sama a Kalaba

Wani dan sandan kwantar da tarzoma da ke sashi na 11  (Mopol 11) da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba ya harbe wani sojan sama a harabar wani banki da ke Layin Ndidem Isong Usong a Karamar Hukumar Kalaba ranar Larabar makon jiyaa. Dan sandan mai suna Williams Enah an kai shi aikin tsaro ne […]

Dan sanda ya kashe sojan sama a Kalaba

Shugaban Yan Sanda na Kasa, Ibrahim Idris

Wani dan sandan kwantar da tarzoma da ke sashi na 11  (Mopol 11) da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba ya harbe wani sojan sama a harabar wani banki da ke Layin Ndidem Isong Usong a Karamar Hukumar Kalaba ranar Larabar makon jiyaa.

Dan sandan mai suna Williams Enah an kai shi aikin tsaro ne a bankin a lokacin hutun Kirsimeti, inda mutane suka rika zuwa na’urar ATM, kuma a lokacin da mutane ke bin layin cirar kudin ne hatsaniya ta kaure a wurin.

Wata majiya da ke wurin lokacin da abin ya faru da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce “Cinkoson mutane ne ya yi yawa, bayan wadansu mutane da suka zo cikin farin kaya da nufin cirar kudi, sai hatsaniya ta kaure. Shi kuma dan sandan da ya ji haka, ya yi kokarin sasanta lamarin, amma abin ya ci tura sai ya yi harbi sama a iska, kuma maimakon harsashin ya yi sama sai ya yi kasa, inda ya samu  sojan saman da ke cikin kayan gida,” inji majiyar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, DSP Irene Ugbo game  ta tabbatar wa Aminiya da aukuwar lamarin, ta ce dan sandan da ya yi harbin yana hannu ana tuhumarsa kan wannan danyen aiki.

Kwammamdan Sojan Sama da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar sun yi wata ganawar sirri domin dakile barkewar rikici a tsakanin jami’an hukumomin biyu. Shi kuma sojan an wuce da shi zuwa asibitin ’yan sanda domin duba lafiyarsa, amma jim kadan sai rai ya yi halinsa.