dan sanda ya kashe wani fursuna a wata kotu da ke Amurka
Wani dan sanda ya harbi wani mutum da ake tuhuma da laifin fashi-da-makami a lokacin zaman wata kotu da ke Amurka bayan da marigayin ya tunkari wani wanda ke ba da shaida a gaban kotun.Mutumin mai suna Siale Angilau ya rasu ne bayan da aka garzaya da shi wani asibiti. Amma kafin mutuwarsa, shi daya […]

Wani dan sanda ya harbi wani mutum da ake tuhuma da laifin fashi-da-makami a lokacin zaman wata kotu da ke Amurka bayan da marigayin ya tunkari wani wanda ke ba da shaida a gaban kotun.
Mutumin mai suna Siale Angilau ya rasu ne bayan da aka garzaya da shi wani asibiti. Amma kafin mutuwarsa, shi daya ne daga cikin mutane 17 da aka fara shari’arsu tun cikin shekarar 2010 inda ake tuhumarsa da laifuffuka 29, da suka hada da da laifin safarar makamai da kuma fashi-da-makami. Wani wanda yake cikin kotun a lokacin da al’amarin ya faru ya ce, dan sandan ya harbi marigayin ne a kirji har sau shida a dai-dai lokacin da ya nufi gurin mai ba da shaida da barazanar kashe shi. Duk da cewa wanda ya nufa din bai samu rauni, amma hukumomi sun umarci da a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro.
Alkalin da ke sauraron shari’ar dai ya dade zaman kotun, inda ya fita daga kotun cikin fushi. Lauyan da yake kare marigayin ya ki ya amsa tambayoyin da manema labarai sukai masa a lokacin da ya bar kotun cikin barcin rai.