Dan sanda ya mutu a harin da `yan garkuwa suka kai ofishin Mothercat
Wani jami`in dan sanda a safiyar yau Laraba ya rasa ransa, bayan da masu garkuwa da mutane su biyar suka kai hari ofishin kamfanin gine-gine na Mothercat da ke unguwar Mando a jihar Kaduna. Majiyarmu ta gano cewa, `yan garkuwan sun yi yunkurin garkuwa da wani babban ma`aikacin kamfanin ne da misalin 5:40 na asuba […]
Wani jami`in dan sanda a safiyar yau Laraba ya rasa ransa, bayan da masu garkuwa da mutane su biyar suka kai hari ofishin kamfanin gine-gine na Mothercat da ke unguwar Mando a jihar Kaduna.
Majiyarmu ta gano cewa, `yan garkuwan sun yi yunkurin garkuwa da wani babban ma`aikacin kamfanin ne da misalin 5:40 na asuba sai jami`an `yan sandan suka dakile harin.
Rahoton na bayyana cewa, an yi nasarar kashe uku daga cikin masu garkuwa yayin da sauran biyun na nan da ransu.