dan sanda ya tsinci jariri a Jihar Nasarawa
A ranar Juma’a makon jiya ne wani dan sanda mai suna Yakubu Abdullahi, ya tsinci wani jariri a daji a kauyen Akurba da ke karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa a lokacin da yake dawowa daga wurin aiki. Bayan ya sanar da hedikwatar ’yan sanda ta Lafiya ne aka karbi jaririn a kai Asibitin kwararru […]

A ranar Juma’a makon jiya ne wani dan sanda mai suna Yakubu Abdullahi, ya tsinci wani jariri a daji a kauyen Akurba da ke karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa a lokacin da yake dawowa daga wurin aiki.
Bayan ya sanar da hedikwatar ’yan sanda ta Lafiya ne aka karbi jaririn a kai Asibitin kwararru na dalhatu Araf da ke Lafiya inda aka tabbatar da lafiyar jaririn, kuma aka mika shi ga wata matar aure.
dan sandan Yakubu Abdullahi ya shaida wa wakilinmu cewa da misalin karfe 6:00 na safe yana komawa gida Akurba daga wurin aiki a kan babur, sai ya shiga daji don biyan bukata, amma sai ya ji kukan jariri a gindin wata bishiya. Ya ce ya ga jaririn a kwance kan ganye a tube yana kuka, kuma ga alama a wurin ya kwana. Ya ce ya sanar da ofishinsu aka tura ’yan sanda suka zo ya ba su jaririn suka kai babban ofishinsu da ke Lafiya.
A Asibitin dalhatu Araf, Babban Likitan dakin yara, Dokta Ozigya Moses ya tabbatar da kai jaririn asibitin inda ya ce daga baya wata matar aure ta je asibitin ta ce tana son jaririn domin ba ta taba haihuwa ba, kuma mutane da dama sun nemi a ba su jaririn. “Bayan shugabanninmu sun yi shawara sai suka ba matar da ta fara cewa tana son jaririn, mai suna Halima Abubakar da ta ce tana zaune a Unguwar Mangu a Lafiya. An karbi lambar wayarta da na mijinta da adireshin gidansu ko mahaifiyar jaririn za ta zo ta ce tana bukatarsa,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ASP Umaru Isma’il ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni rundunar ta soma bincike don gano wacce ta yada jaririn don hukunta ta.