Dan sandan da ya harbe Limami ya shiga hannu
Wani dan sanda mai mukamin sufeta mai suna Okoro Charles da ake zargi da harbe wani limami ya shiga komar ‘yan sanda. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ‘yan sandan ta kame wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu. Bayan da […]
Wani dan sanda mai mukamin sufeta mai suna Okoro Charles da ake zargi da harbe wani limami ya shiga komar ‘yan sanda.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ‘yan sandan ta kame wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu.
Bayan da aka zarge shi da hannu a harbin da ya hallaka wani limami mai suna Fatai Oladipupo a yankin Obabiyi, da ke kan hanyar Igandoa unguwar Ikotun.
Bala Elkana ya ce ana ci gaba da ladabtar da dan sandan da ake zargi, kana idan an same shi da laifi a za mika shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar da ke Yaba kafin daga bisani a gurfanar da shi a kotu.
” Yanzu haka ana ci gaba da bincikar lamarin, kana kwamishinan ‘yan sandan Legas ya mika ta’aziyarsa ga iyalan mamacin, inda ya nemi jama’a su kwantar da hankulan su, domin za a tabbatar an yi adalci” in ji shi
Ya kara da cewa Hukumar za ta ci gaba da bayyana wa al’umma halin da ake ciki akan binciken da suke gudanarwa.