dan sarautar Saudiyya ya kashe Naira biliyan uku a bikin murnar kammala digiri

Wani dan sarautar Saudiyya, tare da bakinsa mutum 60 sun yi bushashar Dala miliyan 20, wanda ya yi daidai da Naira biliyan uku da miliyan 160, a bikin murnar kammala karatun digirinsa, wan da aka gudanar a mashahurin wurin shakatawar nan na duniya da ke Disneyland, kamar yadda yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya […]

dan sarautar Saudiyya ya kashe Naira biliyan uku a bikin murnar kammala digiri
dan sarautar Saudiyya ya kashe Naira biliyan uku a bikin murnar kammala digiri

Wani dan sarautar Saudiyya, tare da bakinsa mutum 60 sun yi bushashar Dala miliyan 20, wanda ya yi daidai da Naira biliyan uku da miliyan 160, a bikin murnar kammala karatun digirinsa, wan da aka gudanar a mashahurin wurin shakatawar nan na duniya da ke Disneyland, kamar yadda yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
Yarima Fahd al-Saud, ya dauki hayar daukacin wurin shakatawar Disneyland na tsawon kwana uku, wato a tsakanin 22 zuwa 24 na watan Mayun, inda aka kiyasta ya kashe a kalla kudin Yuro miliyan 15 ko Dala miliyan 20.41, wato daidai da Naira biliyan uku da miliyan 160.
Wannan biki da aka gudanar a birnin Paris, shi ne karshen yawon shakatawar da yariman ya shirya, inda ya fara da kasar Hong Kong, ya ziyarci wuraren shakatawar da suka hada da na birnin Tokyo da Jihohin Kalifoniya da Florida da ke Amurka, sannan ya karkare a kasar Faransa.
A ruwayar wata jaridar Faransa, ta kuest France, ta bayyana yadda Yarima ya fitar da zayyanar kayan kawa da aka yi amfani da su a wajen bikin; kai hatta yadda aka kawata wurin yana da hannu wajen shirye-shiryen. Ya yiwo hayar ’yan rawa mutum 80.
Shahararrun ’yan wasan majigi da suka hada da Roger da Jessica Rabbit da Aristocats, wadanda suka fito a manyan fina-finai sun halarci wurin bikin.
Yarima Fahd dan marigayi Yarima mai jiran gado, Nayef bin Abdul-Aziz al Saud da matarsa, Gimbiya Maha bint Mohammad bin Ahmad Al-Sudairi ne. Wannan biki na bushasha ya sanya masu yin sharhi a kafafen sadarwa, sun fara bijiro da tambayoyi ga kansu da al’umma, cewa: Mene ne ra’ayinka game da wannan bikin bushasha da Yariman Saudiyya ya yi a wurin shakatawar duniya na Disneyland da ke Paris? Idan kana da Dala miliyan 20 wadda za ka iya sarayar da ita, ko za ka iya shirya biki a wurin da aka fi faranta ran masu shakatawa a wannan duniya?

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda