Dan Sarki a Masarautar Zazzau, Munir Jafaru Ya ajiye Hakimta

Tsohon shugaban hukumar jiragen ruwa ta kasa kuma daya daga cikin fitattun ‘ya’yan sarautar Zazzau, Alhaji Munir Jafaru Ya ajiye mukaminsa na hakimta.

Dan Sarki a Masarautar Zazzau, Munir Jafaru Ya ajiye Hakimta

Tsohon shugaban hukumar jiragen ruwa ta kasa kuma daya daga cikin fitattun ‘ya’yan sarautar Zazzau, Alhaji Munir Jafaru Ya ajiye mukaminsa na hakimta.

Munir Jafaru wanda shi ne Madakin Zazzau kuma Hakimin Basawa, ya sanar da Masarautar Zazzau cewa ajiye mukaminsa na matsayin hakimta bisa ra’ayin kashin kansa.

A wata takardar da jami’in hulda da jama’a na Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya sanya wa hannu ta cde hakimin ya ajiye mukaminsa ne ta wata takarda da ya rubuto wa masarautar a ranar 29 ga watan Yuli, 2023.

Takardar ta ce ” Sakamakon karbar takardar ajiye Hakimta da Madakin Zazzau, Alhaji Muhammadu Munnir Ja’afaru
ya rubuto mai dauke da kwanan wata 29 ga watan Yuli 2023, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli nan take ya amince da takardar.

“Ba tare da bata lokaci ba ya amince da nadin Akitet Haruna Abubakar Bamalli, Barde Kerarriya kuma Hakimin Zangon Aya a matsayin Sabon Hakimin gundumar Basawa.”

Takardar da Masarautar Zazzau din ta fitar ba ta yi karin bayani ba a kan dalilin tsohon hakimin ya ajiye mukaminsa ba.

Duk kokarin da wakilin Aminiya ya yi na jin ta bakin Madakin Zazzau Alhaji Muhammadu Munnir Ja’afaru, hakan bai yiwu ba kasancewa ba ya gari kuma lambar wayarsa ba ta shiga.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos