‘dan sarki da ’yan mata hudu’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau kuma zan kawo muku labarin ‘dan sarki da ‘yan mata hudu’. Labarin ya kunshi yadda saukin kai ke janyo nasara. A sha karatu lafiya. Akwai wani dan sarki ne da ya dawo daga kasar waje. Kuma […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau kuma zan kawo muku labarin ‘dan sarki da ‘yan mata hudu’. Labarin ya kunshi yadda saukin kai ke janyo nasara. A sha karatu lafiya.
Akwai wani dan sarki ne da ya dawo daga kasar waje. Kuma mahaifinsa na son ya je gidan Hajiya Delu don ya auri daya daga cikin ‘ya’yanta kasancewar ya yaba da irin tarbiyarsu. Da farko dai dan sarki bai so hakan ba amma ganin cewa mahaifinsa ba abin da bai masa ba a rayuwa, sai ya yanke shawarar ya je don ya gansu.
dan sarki ya hada baki da kanwarsa cewa zai je gidan Hajiya Delu amma a matsayin mai aiki ta wannan hanyar ce kawai zai iya gane ainihin tarbiyar ‘yan matan da kuma hankalinsu.
Da ya isa gidan ya roki Hajiya Delu da ta taimaka masa koda da shara da wanke-wanke ne.
A cikin mata hudun da ya kwashe a gidan dan sarki ya lura cewa ita babbar tana da saurin fushi domin ya kona mata kaya a lokacin da yake yi mata guga inda ta kwashe shi da mari.
Ta biyu kuma buri ya yi mata yawa. Kullum burinta shi ne ta auri dan sarki sai dai tana da yawan son samari ga kuma yawan yawo.
Ta ukun ba ta damu da auren dan sarki ba, ita dai mai karamar buri ce kuma ba ta da raini. Domin akwai ranar da ta yi ado za ta fita, dan sarki kuma yana wanke mota sai ya watsa mata ruwa ba tare da saninsa ba da ta fusata sai ta zage shi amma daga baya ta ba shi hakuri.
Na hudun kuma ba a sanya ta a lissafi domin mata-maza ce. Sai son yin shigar maza da kuma wasa da maza.
Da dan sarki ya koma gida sai ya gaya wa mahaifinsa cewa ya samu matar aure. Daga nan aka shaidawa Hajiya Delu neman auren ‘yarta ta uku. Nan da nan ta amince aka yi auren. Daga nan sauran matan suka yi matukar da-na-sanin abin da suka aikatawa dan Sarki. Sai makon gobe in Allah Ya kaimu.
Taku; Gwaggo Amina Abdullahi.