dan Saudiyya ya bukaci matarsa ta yi masa bulala a kotu

Wani Balaraben Saudiyya ya bukaci matarsa ta yi masa bulala, bayan da kotu ta yanke masa hukuncin bulala 30, saboda cin zarafin matarsa. Matar wannan Balarabe ita ta kai wa kotu karar, don haka kotu ta bukaci ya roki afuwarta, sannan za a yi masa bulala 30, kamar yadda wata jarida Al-Watan ta ruwaito.A lokacin […]

dan Saudiyya ya bukaci matarsa ta yi masa bulala a kotu
dan Saudiyya ya bukaci matarsa ta yi masa bulala a kotu

Wani Balaraben Saudiyya ya bukaci matarsa ta yi masa bulala, bayan da kotu ta yanke masa hukuncin bulala 30, saboda cin zarafin matarsa. Matar wannan Balarabe ita ta kai wa kotu karar, don haka kotu ta bukaci ya roki afuwarta, sannan za a yi masa bulala 30, kamar yadda wata jarida Al-Watan ta ruwaito.
A lokacin da mutumin ke rokon afuwar a wurin matarsa a cikin kotun, sai ya ce mata ta dauki bulala ta zane shi sau 30, kamar yadda jaridar kullum ta Al Anba ta ruwaito daga majiyarta, a hukumar shari’a ta Saudiyya.
“Ke ya kamata ki yi mini bulala,” mutumin ya fada wa matarsa. “Ko da za ki wuce bulala 30 din da kotu ta yanke mini zan amince, saboda muhimmin al’amari dai shi ne ki kasance cikin farin ciki,” inji shi.
Ganin yadda mutumin ya jajirce wajen neman afuwar, sai matarsa ta bayyana wa kotu cewa ta yafe masa.
Ta ce, ta amince da alkawarin da ya dauke na kula da ita yadda ya dace, zai kuma rika kyautata mata, musamman ma tunda suna da ’ya’ya a tsakaninsu, kamar yadda jaridar ta ruwaito.