dan Saudiyya ya bukaci wayar iPhone 6 a matsayin sadakin ’yar uwarsa

Wani dan kasar Saudiyya ya bukaci a biya ’yar uwarsa sadakin na’urar wayar hannu iPhone 6. An dai bukaci angon ya kawo sabuwar wayar hannu, wadda har yanzu bat a shigo kasuwannin Saudiyya ba, matukar yana son a ci gaba da udanar da harkokin bikin aurensa.Wannan ango an gindya masaa sharadin auren yarinyar ne, inda […]

dan Saudiyya ya bukaci wayar iPhone 6 a matsayin sadakin ’yar uwarsa
dan Saudiyya ya bukaci wayar iPhone 6 a matsayin sadakin ’yar uwarsa

Wani dan kasar Saudiyya ya bukaci a biya ’yar uwarsa sadakin na’urar wayar hannu iPhone 6. An dai bukaci angon ya kawo sabuwar wayar hannu, wadda har yanzu bat a shigo kasuwannin Saudiyya ba, matukar yana son a ci gaba da udanar da harkokin bikin aurensa.
Wannan ango an gindya masaa sharadin auren yarinyar ne, inda aka bukaci lalali sai ya bata sabuwar wayar hannu ta iPhone 6 da zarar ta shigo kasuwa a kasar Saudiyya, don a samu ci gaba da gudanar da bikin aurensu. dan uwar yarinyar, ya shafe bukatar mahaifinsu na cewa a ba ta wasu ’yan kudi kadan a amtsayin sadakin aurenta, kamar yadda Jaridar Kuwait Al anba ta ruwaito.
Al’adar biyan sadaki a kasashen Larabawa na yankin Asiya na da tushe tun fil azal, amma duk da kiran da malamai ke yin a a saukakata, ta hanyar bayar da kyaututttuka masu sauin kudi, iyala da dama sun jajirce kan sai sun karbi kudi mai tsoka kafin su aurar da ‘’yar su.
Matasan yankin tekun Fasha, tuni suka jajirce wajen ganimn an rika biyan sadaki mai sauwi, amma duk da haka rikon da aka yi wa al’ada da kibar darajar iyalai da kabilu sun ki amincewa da wnanan manufa.
“Mun sha jin abubuwa irin wadannan, amma iPhone 6, wadda ko kasuwanni ba ta shigo ba, wannan al’amari ya zama bambarakwai,” a cewar Sa’ud Ahmad, wani ma’aikaci a kasar Bahrain. “Akwai bukatar mun bunkasa al’adu, ta yadda wani ba zai yi amfani da aure don samun kyaututtuka ko cin kazamar riba. Idan da ni ne wanan angon, da na tunkari dan uwanta mu daddale,” inji shi.