dan Saudiyya ya gindaya wa matarsa dokoki saboda gasar cin kofin kwallon duniya

Wani dan kasar Saudiyya mai tsananin son kwallon kafa ya gindaya wa matarsa wasu dokoki da za ta kiyaye har a kamala gasar cin kofin kwalon kafa ta duniya, matukar tana son aurensu ya ci gaba da dorewa.Wkannan magidanci ya rubuta dokoki, ya lika su a wurare dabandaban a gidan, ta yadda matarsa za ta […]

dan Saudiyya ya gindaya wa matarsa dokoki saboda gasar cin kofin kwallon duniya
dan Saudiyya ya gindaya wa matarsa dokoki saboda gasar cin kofin kwallon duniya

Wani dan kasar Saudiyya mai tsananin son kwallon kafa ya gindaya wa matarsa wasu dokoki da za ta kiyaye har a kamala gasar cin kofin kwalon kafa ta duniya, matukar tana son aurensu ya ci gaba da dorewa.
Wkannan magidanci ya rubuta dokoki, ya lika su a wurare dabandaban a gidan, ta yadda matarsa za ta rika ganinsu, kuma ba za ta manta ba, kamar yadda shafin sadarwar Ain Al Yawm ya ruwaito a Litinin din makon jiya.
Daga cikin dokokin, ya bukaci matarsa ta sanar da shi a duk lokacin da take son ziyarar ’yan uwanta ko kawaye, sa’o’I biyu kafin a fara wasa. Sannan zuwa cefane a manyan katuna, shi ma sai ranakun da babu kwallo, a cewar mijin. Wannan dopkoki dai sun tsaurara ga wannan mata, domin mata a Saudiyya an hana su tuka mota, don haka ko di su hau tasi, ko kuma mijinsu ya tuka su ya kai su duk inda za su.
Maigidan ya gargadi matarsa da kada ta sake ta yi wani tsokaci a duk lokacin da yake bakin ciki ko murnar cin wasa.
“Ta yiwu in yi jifa da na’urar laluluben tashoshi da kunna talabijin a lokacin da nike cikin damuwa,  don haka ba na son cutar da ke. Ina son ci gaba da ririta irin kyawun da Allah ya yi miki (kada rauni ya rage mata farashi),” kamar yadda yake rubuce a jerin dokokin.
“A duk lokacin da ake buga wasa, ina so ki zama cikin shirin ganin duk abin da na aikata wajen kwarzanta kungiyar kwallon da nike kauna. Zan iya yin kuri da barazana, duk ba na so su tsorata ki,” inji shi.
Ya bayyana cewa yana son Italiya ta ci kofin kwallon. Magidancin dia ya bayyana cewa, wadannan dokoki za su daina aiki ne da zarar an hura usur din kamala gasar wasan a ranar 13 ga Yulin bana.
Larabawan Saudiyya na matukar son kwallon kafa, don har ta kai ga na baza wani hoto a shafukan sadarwa da ke nuni da yadda wani dan Saudiyya ya mayar da dakinsa siffar filin wasan kwallo, sannan ya kawata shi da tutocin kungiyoyin wasan kwallon kafa da yake kauna.