dan Segun Odegbami zai angwance

Stephen, dan shahararren dan kwallon Green Eagles Segun  Odegbami zai angwance. A wata sanarwar da angon da kuma amaryar suka fitar a kafar sadarwarsu ta Twitter a ranar Talatar da ta wuce, sun bayyana auren zai gudana ne a ranar 14 ga watan Mayun 2016 a Amurka.Stephen dai shi ne na biyu a cikin ’ya’yan […]

dan Segun Odegbami zai angwance
dan Segun Odegbami zai angwance

Stephen, dan shahararren dan kwallon Green Eagles Segun  Odegbami zai angwance.
A wata sanarwar da angon da kuma amaryar suka fitar a kafar sadarwarsu ta Twitter a ranar Talatar da ta wuce, sun bayyana auren zai gudana ne a ranar 14 ga watan Mayun 2016 a Amurka.
Stephen dai shi ne na biyu a cikin ’ya’yan da Segun Odegbami ya haifa.  Kwanan nan ya kammala karatunsa a wata Jami’a da ke Amurka kuma ana kyautata zaton a can Amurka zai zauna da amaryar idan ya aureta.
Ita ma amaryar tasa wacce ba a ambaci sunanta ba, rahoton ya nuna a can Amurka take da zama.  Hasalima a can suka hadu inda suka dade suna soyayya kafin su yanke shawarar yin aure a wannan shekara.
Idan za a iya tunawa, Segun Odegbami yana daga cikin zaratan ’yan kwallon Green Eagles kafin a sauya mata suna zuwa Super Eagles.  A wancan lokaci ana yi masa kirari ne da “Mathematical” watau mai lissafi ganin yadda ya zama gwani wajen gudu da kwallo a kan layi ba tare da ta fita ba.
Bayan Segun Odegbami ya yi ritaya daga kwallo ne ya zama mai yin sharhi a kan al’amurran kwallo a kafofin watsa labarai ciki har da jaridar Daily Trust ta Turanci da ke fitowa a duk ranar Asabar (Daily Trust on Saturday).

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa