dan shekara 10 ya kwakwule idon kada don ceton akuyarsa
Wani yaro shekara 10 a Bihar da ke kauyen Bhediari Tola a Yammacin champaran ya yi artabu da kada, inda ya kwakwule mata idon ya ceci akuyarsa. Rahotanni sun yi nuni da cewa yaron dan shekara 10, mahaifiyarsa ta umarce shi da ya rika kiwon awaki a duk sa’adda da ya dawo daga makaranta; yana […]
Wani yaro shekara 10 a Bihar da ke kauyen Bhediari Tola a Yammacin champaran ya yi artabu da kada, inda ya kwakwule mata idon ya ceci akuyarsa. Rahotanni sun yi nuni da cewa yaron dan shekara 10, mahaifiyarsa ta umarce shi da ya rika kiwon awaki a duk sa’adda da ya dawo daga makaranta; yana cikin wannan aiki ne , sai wata rana kawai kada ta fito daga rowan da yake shayar da dabobi ta kama akuya daya.
Wannan yaro dan aji shida na Firamare ya yi fafutikar ceton akuyarsa, kawai kadar ta saki akuyar ta kama hannunsa, kafin agutsure hannun shi kuwa sai ya kwakule mata ido. Jin zafin abin da ya yi wannan kada, sai kawai ta sake shi, ta fada cikin ruwa.
Wadanda al’amarin ya auku a gabansu, sun bayyana cewa, kadar ta ji haushin abin da yaron ya yi mata, sai ta saki akuyar, ta kama hannun yaro. Yaron dai ya zubar da jini.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa babu wani daga cikin mazaunan kauyen da yi katabus wajen taimakon yaron, a tsawon minti 30 da suka yi suna fafatawa.