dan shekara 10 ya saci rabin miliyan a Jigawa

Wani yaro dan shekara 10 (an sakaya sunansa) ya shiga hannun jami’an tsaro na Nigeria Security and Cibil Defence Corps (NSCDC) reshen Jihar Jigawa bisa zarginsa da satar Naira dubu 500 (rabin miliyan).Kamfanin Dilancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Kwamandan NSCDC na jihar Malam Muhammad Gidado, yana shaida wa manema labarai a Dutse a […]

dan shekara 10 ya saci rabin miliyan a Jigawa

????????????????????????????????????

Alhaji Sule Lamido Gwamnan Jihar JigawaWani yaro dan shekara 10 (an sakaya sunansa) ya shiga hannun jami’an tsaro na Nigeria Security and Cibil Defence Corps (NSCDC) reshen Jihar Jigawa bisa zarginsa da satar Naira dubu 500 (rabin miliyan).
Kamfanin Dilancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Kwamandan NSCDC na jihar Malam Muhammad Gidado, yana shaida wa manema labarai a Dutse a ranar Litinin da ta gabata cewa an kame wanda ake zargin ne a ranar Larabar makon jiya a karamar Hukumar Kiyawa da ke jihar.
Malam Gidado ya ce an sace kudin ne daga gidan mahaifiyar wanda ake zargin wadda take zaune a karamar Hukumar kuma kudin adashe ne da uwar take wa uwar taru.
Ya ce an kama yaron ne bayan da mutanen gari suka kai rahoto kan yadda suka ga yana facaka da kudi.
Kwamandan ya ce an kwato wani keken-tsere da kudinsa ya kai Naira dubu 45 da kuma tsabar Naira dubu 250 daga yaron. Kuma ya ce ana ci gaba da bincike a kan lamarin.