Dan shekara 12 yana goya abokinsa mai nakasa zuwa makaranta shekaru 6
Masu iya magana na cewa, abokin kirki shi ne wanda zai taimaka maka a lokacin da kake bukatar taimako. Wani dalibi mai suna Du Bingyang mai shekara 12, ya shafe shekara shida yana goya abokin karatunsa mai nakasa mai suna Zhang Ze zuwa makarantarsu komai ruwa komai zafin rana. Zhang Ze yana zuwa ajin karatu […]
Masu iya magana na cewa, abokin kirki shi ne wanda zai taimaka maka a lokacin da kake bukatar taimako.
Wani dalibi mai suna Du Bingyang mai shekara 12, ya shafe shekara shida yana goya abokin karatunsa mai nakasa mai suna Zhang Ze zuwa makarantarsu komai ruwa komai zafin rana.
Zhang Ze yana zuwa ajin karatu na tsawon shekara shida ba tare da wata matsala ba, saboda abokin karatunsa Du Bingyang yana goya shi a bayansa zuwa makaranta kullum.
Du Bingyang kuma yana taimaka wa abokinsa wajen nemo musu abinci da shiga wasu ajujuwa don daukar darasi.
Kafafen labarai na Sichuan Online da Dinhua, sun wallafa labari da hoton aminan biyu da ke karatu a wata makaranta da ke birnin Meishan a Lardin Sichun da ke Kudu maso Yamma na kasar China, a watan jiya.
Du ya fi abokinsa Zhang tsawo da karfi, kuma ya bayyana wa manema labarai cewa, ya zabi ya zamarwa abokinsa jagora wanda hakan yana nisahadantar da shi.
Du, ya kara da cewa, abu ne mai wahala ya kyale abokinsa Zhang cikin kunci.
Du, ya ce nauyinsa ya kai Kilo 40 yayin da nauyin abokinsa ya kai kilo 25 don haka zai iya daukarsa ba tare da wata matsala ba.
Zhang, ya ce bai da kalmar da zai iya gode wa Du, saboda irin taimakon da yake yi masa.
“Du Bingyang shi ne amintaccen abokina a koyaushe, muna karatu tare, mu tattauna tare, mu yi wasa tare, ina godiya kan dawainiyar da yake yi da ni kullum,” kamar yadda Zhang ya fada wa kafar labarai ta Sichuan Online.
Du da Zhang suna aji shida na makarantar firamare ta birnin Hebazi a Karamar Hukumar Kingshen.
Binciken da likitoci suka yi ya bayyana cewa, Zhang yana dauke cutar laka ce, wadda ake kira ‘rag doll’ kuma ya hadu da wannan cuta ce tun yana da shekara hudu da haihuwa.
Cutar da take damun Zhang masu bincike na kiranta da ‘myasthenia grabis,’ wadda ta yi sanadiyyar rashin aikin kafafunsa ta yadda bai iya tafiya da kafafun.
Abin mamakin Zhang bai taba fashin zuwa makaranta ba tun daga ajin farko, saboda tun haduwarsu da Du yana taimaka masa wajen goya shi zuwa makaranta, daga shekarar farko zuwa shekara shida da suke tare.
A lokacin da Du yake ganawa kafar labarai ta Chengdu Economic Channel, ya ce aikinsa ne ya taimaka wa masu bukatar taimako.
Du, ya ce: ‘Na fi Zheng girma, ina tunanin idan ban taimake shi ba, wa zai taimake shi? Wannan taimakon da nake yi wa Zheng bai zama abu mai sauki ba.
Misali, mutum biyu za su iya kai minti uku daga aji zuwa ban-daki mai nisan mita 70 (kafa 230).
Wannan shi ne kadan daga cikin daukar Zheng da Du ke yi idan suna tare, wani lokacin yana rike hannuwansa.
Idan abokan sun tarar da matakala a hanya sai Du ya goya Zheng a bayansa.
Du, a koyaushe yana taimakon Zheng wajen zuba masa ruwa a gorarsa, sannan ya kai shi ban-daki.
Taimakon aboki irin wannan na yau da kullum yana bukatar juriya da hakuri wajen aiwatarwa.
Zhang yana samun taimakon Du shekara uku da suka gabata da wani yaro.
Daya daga cikin malaman firamaren ya ce, a lokacin da Zhen yake aji uku wadansu abokansa da suke taimaka masa sun kaurace masa saboda rashin lokacin da suka ce, suna fuskanta na yin karatu.
Malamin firamaren ya bayyana wa Sichuan Online cewa, tun lokacin da Du yake taimakon Zheng bai taba yin korafi a wajen malamansa da sauran abokan karatunsa. Du, ya nada kokari matuka.
Ba kawai mahaifiyar Du, ba ne ta san taimakon da yake yi wa jama’a ba.
Mahaifiyar Du, ta ce, “Dana mai jin kunya ne bai taba zuwa ya fada mini yadda yake gudanar da harkokinsa ba, sai dai inji a wajen jama’a kawai.”
Abin da mahaifiyar Du, ta sani game da danta shi ne babban burin Du a rayuwa nan gaba shi ne ya rika taimakon mabukata na kusa da shi da kuma al’ummar gari.