Dan shekara 14 ya zama matukin jirgin sama
Ranar 30 ga Agustar da ta wuce Mansoor dan shekara 14 ya tuka jirgin sama a Cessana da ke kasar Hadaddiyar daular Larabawa, al’amarin kuwa ya faru bayan da ya samu horo na tsawon sa’o’i 25. Tuka jirgin saman da ya yi ya ba shi damar shiga jerun masu karancin shekaru da ke tuka jirage. […]
Ranar 30 ga Agustar da ta wuce Mansoor dan shekara 14 ya tuka jirgin sama a Cessana da ke kasar Hadaddiyar daular Larabawa, al’amarin kuwa ya faru bayan da ya samu horo na tsawon sa’o’i 25. Tuka jirgin saman da ya yi ya ba shi damar shiga jerun masu karancin shekaru da ke tuka jirage.
Yaron dalibi ne a Sharjah. Kuma Mansoor Anis ya fara samun horo ne tun yana da shekara bakwai, a lokacin da aka fara koya masa dabarun tukin a cikin kwamfuta, inda kawunsa dan asalin New Delhi ta Indiya, wani kwararren matukin jirgin sama ya yi aiki da kamfnain sufurin jiragen sama na Indiya mai zaman kansa.
“Da irin wannan masarafar kwamnfuta kawunsa ya fara ba shi horon tukin jirgin sama,” kamar yadda ya fada wa jaridar Khaleej Times. “Tun daga lokacin na damfaru da sha’awar al’amarin,” inji shi.
Lokacin da Mansoor ya kai shekara 13 sai ya ji yana son zama matukin jirgin sama, don haka cikin shekara guda da ya tafi kasar Canada da mahaifiyarsa sai ya fara samun horo a makarantar horar da matukan jirgi ta AAA Abiation Flight Academy da ke birnin Langley a yankin British Colombia.
A cewar Mansoor shugaban bayar da horo a makarantar (CFI) ya dan fara tunanin ka da ya dauki wannan karamin yaro a matysayin dalibinsa, amma sai ya lura cewa Mansoor na da matukar sha’awar tukin jirgin sama.
“Da farko babban jami’in bayar da horo (CFI) ya dan yi takatsantsan wajen daukata. Amma tukin farko da na yi, sai ya yi matukar gamsuwa, tare da zimmar son koyar da ni, saboda ya gano cewa nasan abubuwa da dama kuma ina koyo cikin sauri,” inji shi. “Sai dai lamarin babu sauki. Domin tashin jirgin sama ya sha bamban da tsarin koyarwar kwamfuta.
“Abin da na koya daga kawuna ya yi matukar taimaka mini,” inji Mansoor. “Alal misali, akwai wasu tsare-tsare da aka fasalta su, wadanda suka yi kama da kayan aiki, da ya koya mini na rike su.”
Ranar 30 ga Agustan bana sai Mansoor ya tuka jirgi shi kadai a cibiyar horo ta Cessna 152
“Na dan ji tsoro, amma a shirye nike in tashi. Na yi matukar farin ciki kan al’amarin,” inji shi. “Jirgin ya tashi cikin minti 10 zuwa 12. Na dan yi dar-dar lokacin da na zo sauka . al’amarin na da wahala. Na kwashi dimbin lokacin kafin in koya da gaske.”
Da dawowarsa Sharjah cikin wanan makon, Mansoor ya ce yana cike da farin ciki da kwarin gwiwa kan yabon da ya samu daga abokansa da iyayensa.
“Iyayena na alfahari da ni, kuma abokaina sun yi farin ciki da ni,” inji shi. “Yanzu suna son in koma makaranta.”
A cewar Mansoor da iyayensa, ya kafa tarihin ne inda ya koyi tukin a mafi karancin sa’o’i, sabanin yadda aka taba samu a da na sa’a 34 ga karamin matukin jirgin sama mai karancin shekaru.
Ali, mahaifinsa ya ce tuni suka cika takardun da za su ba shi damar shiga jerin wadanda kundin shahararrun al’amuran duniya Limca Book of records ya tattara bayanai a kansu, wanda ya fi mayar da hankali kacokam kan Indiyawa da ke kasarsu da wadanda ke kasashen waje.
Nan gaba Mansoor ya ce yana da tabbacin zai tuka jirgin sama amatsayin kwararren matuki.
“Ina son zama matukin jirgin sama,” a cewarsa. “Burina in yi aiki da jiragen Emirates da Etihad.”
Mansoor ya shawarci matasan da ke hankoron tuka jirage su yi shawagi a sararin samaniya, inda ya ce: Lokacin da kuke tashi sama, ka da ku ji tsoro. Lamarin na da dadin sha’ani, inji shi. “Kada a nuna gazawa nan da nan.”