dan shekara 20 ya yi lalata da akuya a Jigawa

Kotun Majistare ta Biyu da ke Dutse fadar Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Auwalu Sani Balago ta tura wani matashi mai suna Khamisu Audu baranda gidan maza na tsawon mako biyu kafin a ci gaba da shari’ar da ake masa na zargin yin lalata da akuya a dajin Baranda a ranar Talatar da ta […]

dan shekara 20 ya yi lalata da akuya a Jigawa
dan shekara 20 ya yi lalata da akuya a Jigawa

Kotun Majistare ta Biyu da ke Dutse fadar Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Auwalu Sani Balago ta tura wani matashi mai suna Khamisu Audu baranda gidan maza na tsawon mako biyu kafin a ci gaba da shari’ar da ake masa na zargin yin lalata da akuya a dajin Baranda a ranar Talatar da ta gabata.
Mai sharia Auwalu Balago ya ce saboda wanda ake tuhumar ya musanta laifin da ake zarginsa ne ya tura shi gidan maza domin ’yan sanda su samu damar kammala bincike a kansa tare da gabatar da shaidunsu.
Lauyar gwamnati mai gabatar da kara a gaban kotun Hajiya Fatima ta ce ’yan sanda suna tuhumarsa da laifin satar akuyar ce da kuma yin lalata da ita akuyar saboda haka ta bukaci a mayar da shi gidan yari domin ’yan sanda su samu damar kammala bincike.
Khamisu Sani ya shaida wa manema labarai cewa ba satar akuyar ya yi ba, amma ya yi kokarin yin lalata da akuyar ne aka kama shi.
Ya ce ba ya satar awaki amma ya jima yana yin lalata da awaki domin yana samun biyan bukata daga wajan dabobi fiye da yin amfani da mata. Ya ce abin da ya sa ba ya amfani da mata saboda yana gudun ya samu matsala da mutane kada a yi masa hukunci sabanin yadda yake tunani.
Ya ce Dagacin Baranda ne ya kama shi yana kokarin yin lalata da akuyar amma bai kai ga aikatawa ba aka kama shi aka mika shi ga ’yan sanda daga nan kuma aka gabatar da shi a gaban kotu. Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 3/3/na 2014 domin ci gaba da shari’ar.
A wani labarin kuma jami’an tsaro na farin kaya da ake kira Sibil Difens su kama sami wani mai shekara 40 mai suna Malam Nasiru Sani da ke karamar Hukumar babura bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekara 20 (an sakaya sunanta) ciki, inda ake zargin Nasiru Sani da budurwar da hada baki su zubar da cikin mai wata shida tare da binne dan tayin a wani gida.
Yanzu haka likitoci sun dukufa don gano gawar jaririn da ake zargin sun kashe kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.