dan shekara 29 ya makale wa budurwarsa ’yar shekara 62
Wani matashi dan shekara 29, mai suna Zhu ya bukaci budurwarsa ’yar shekara 62 ta dawo bayan da ta bace masa a cikin watan Oktobar bana. Kuma wannan shi ne karo na biyu da matar mai lakabin Ms. Wu ta bace. “Ita ce budurwata ta farko a rayuwa,” inji Zhu. “Ba taba mu’amala da mace […]
Wani matashi dan shekara 29, mai suna Zhu ya bukaci budurwarsa ’yar shekara 62 ta dawo bayan da ta bace masa a cikin watan Oktobar bana. Kuma wannan shi ne karo na biyu da matar mai lakabin Ms. Wu ta bace.
“Ita ce budurwata ta farko a rayuwa,” inji Zhu. “Ba taba mu’amala da mace ba kafin haduwata da ita. Mun yi alkawarin aure, mun zauna tare har abada. Bambancin shekaru ba matsala ba ce,” inji shi.
Wadannan saurayi da budurwa sun hadu ne a wani hadin ‘’yar cankar ma’aurata da ake gudanarwa a kasar gsa masu son su yi aure. Bayan cankarsu ta zabo su, sai suka fara nuna soyayya da kaunar juna.
Da farko dai cikin Afirilun bana, Wu ta koma gida wajen iyalanta, wadanda suka nuna adawarsu da wannan soyayya. Zhu kuwa ya bi ta, don ganawa da masoyiyarsa, amma danta ya kore shi.
A wani hoton bidiyo da aka baza a shafukan intanet, an jiwo Zhu yana cewa: “Mahaifiyarka ta ce tana sona.
Shi ma tsohon mijin Wu day a samu labarin wannan soyayya sai kawai ya shiga tashar talabijin yana rokon masoyiyarsa. A cbikin wannan faifan bidiyon, an jiwo mutumin yana cewa: “Mun rabu da ita, amma wani mutum yana zuwa wajena ya tambayi inda Wu take.”
Duk da tserayyar shekaru 33 da ke tsakaninsu, Zhu ya ce suna cike da farin ciki, sai dai al’umma na matukar sa musu ido. Kuma abokan Wu na zargin saurayinta d ahaifar da rudani.
“Ka cika binta duk inda ta je, shi yasa ta gudu,” a cewar abokin Zhu. Labarin wadannan ma’aurata ya bazu a shafukan intanet, inda mutane suka yi ta sharhi a kani. A sharhin mutanen: “Ko yaya gibin da ke tseakanin jinsi yake a kasar Sin?” wasu kuwa cewa suka yi:” wannan shi ne labara mafi ban dariya da shirme na shekarar 2015, amma sun bayar da shawarar cewa kada mutum ya cika matsin lamba wajen tarairayar budursa. Akwai kuma wadanda suka yi wa matashin lakabi da sunan matashin karamin yaro, ya kuma tsananta wajen makale mata.