Dan shekara 38 ya zama shugaban majalisar Osun

Adewale Egbedun mai shekara 38 ya ce zai yi aiki tukuru don ciyar da al’ummar jihar gaba.

Dan shekara 38 ya zama shugaban majalisar Osun

An zabi dan wani dan shekara 38 mai suna Adewale Egbedun a matsayin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Osun.

’Yan majalisar sun zabi Egbedun da ke wakiltar mazabar Odo-Otin, domin jagorance su ne bayan da Ibrahim Abiola daga mazabar Irewole/Isokan ya gabatar da shi sannan Areoye Samuel, wani mamba ya mara masa baya.

Da yake gabatar da jawabinsa na farko jim kadan bayan zaben sa a matsayin shugaban majalisar ta takwas, Egbedun ya tabbatar wa al’ummar Osun cewa majalisar za ta yi kokarin ganin an samu cigaba na gari a jihar.

“Ina tabbatar wa al’ummar Jihar Osun cewa wannan majalisa za ta yi musu wakilici bisa gaskiya da rikon amana.

“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kare hakkin ’yan kasa da dorewar shugabanci nagari da aiwatar da ayyukan cigaba da sanya ido a kan bangaren zartarwa da hukumomi da sauransu,” in ji shi.

Ya kuma bai wa Gwamna Ademola Adeleke tabbacin biyayya da goyon bayan ’yan majalisar a yunkurinsa na samar da shugabanci nagari a jihar.

Ya ce, “Gwamna zai same mu a matsayin masu gaskiya, da goyon baya wajen gudanar da aikinmu na majalisar.

“Zan yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamna da ya mika wa wannan majalisa, sabbin kudurorin zartarwa nasa kan batutuwan da suka shafi jama’a.

“Muna sane da cewa gwamnan ya kammala wasu daftarin kudirorin doka don tafiyar da manufofinsa. Muna fatan za a gaggauta bin diddigin wadannan yunkuri domin al’ummar Osun su ci gajiyarsu.

“Na kuma yi amfani da wannan damar wajen sanar da cewa shugabanninmu za su tattara tare da duba duk wasu kudurorin kudi na karshe da gwamnatin mai barin gado ta amince da su.”

Lakurawa sun tsere bayan sojoji sun ragargaje su a Kebbi

NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga

’Yan bindiga sun lalata tashar wutar lantarkin da ake ginawa a Kogi

Trump ya bai wa Elon Musk muƙami a Gwamnatin Amurka