Dan shekara 70 ya yi wa ’yar shekara 8 fyade a Benin

A karshen makon jiya ne wani tsoho mai shekara 70, Muhmmadu Maidoya ya yaudari wata yarinya ’yar shekara takwas (an sakaya sunanta) da Naira goma, ya shigar da ita dakin da yake haya a garin Benin, Jihar Edo, ya yi mata fyade.Wannan lamarin ya faru ne a layin Odiye da ke garin Benin. Kamar yadda […]

Dan shekara 70 ya yi wa ’yar shekara 8 fyade a Benin
Dan shekara 70 ya yi wa ’yar shekara 8 fyade a Benin

Muhammadu Maidoya, dan shekara saba’in da ake tuhuma da yi wa yarinya fyadeeA karshen makon jiya ne wani tsoho mai shekara 70, Muhmmadu Maidoya ya yaudari wata yarinya ’yar shekara takwas (an sakaya sunanta) da Naira goma, ya shigar da ita dakin da yake haya a garin Benin, Jihar Edo, ya yi mata fyade.
Wannan lamarin ya faru ne a layin Odiye da ke garin Benin. Kamar yadda shaidu da ido, mutanen wannan unguwa suka bayyana kuma sun ce wannan tsohon da aka kame, dan asalin garin Azare ne da ke Jihar Bauchi kuma sun ce dubunsa ta cika ne a safiyar Asabar da ta gabata, daidai da misalin karfe shida da rabi.
Sun ce Maidoya ya ga wannan yarinyar tana wucewa zuwa sayo koko, kawai sai ya kira ta, kamar wani abin arziki zai yi mata ko zai aike ta ta sayo masa wani abu. Da zuwan ta ya ba ta Naira goma, sai ya shigar da ita daki. A wannan lokacin ne ya gama mata lalatar ta lallabo ta koma gida, ta shiga ta samu iyayenta tana cikin wani yanayi a galabaice. Ganin haka iyayenta suka sa ta a gaba ta, kai su wurin wannan mutum, wanda ta ce ya yi mata fyaden.
Mahaifiyar yarinyar ta ce: “Mun same shi, ko da ya gan mu tare da yarinyar, sai ya yi shirin zai gudu. Ganin hakan sai muka sa aka buga waya ga shugaban ’yan banga na nan unguwar, Alhaji Muhammadu S. Katsina, domin ya kawo mana gudunmowa cikin gaggawa kuma bai bata lokaci ba, ya turo ma’aikatansa suka zo suka kame shi suka tafi da shi ofishinsu.
Shugaban ’yan banga ya tabbatar wa wakilinmu cewa sun kame wanda ake zargin amma ya ce suna shirin mika shi ga hukumar ’yan sandan shiyyar. “Ba za mu aje shi a wurinmu ba. Za mu kai shi mu mika wa ’yan sanda.”
Aminiya ta kalato cewa mutumin da ake zargin, bayan ya shiga hannu ya fada wa ’yan banga a ofishinsu cewa lallai ya aikata fyde ga wannan yarinyar amma ya ce yana neman afuwa ga iyayenta.
’Yan Banga, kamar yadda bayani ya tabbatar, sun dauki yarinyar suka kai ta wani asibiti mai zaman kansa a cikin garin Benin, domin neman taimakon gaggawa kuma babban likita na asibitin, Dokta Duke ya karbe ta, ya yi bincike ya tabbatar da cewa an yi wa yarinyar mummunan rauni a sakamakon wannan fyade; dalili ke nan ya sa likitan ya b ata gado domin jinyarta.
Har zuwa lokacin hada wannan labara, ba a samu karin bayani ba daga hukumar ‘’yan sanda, domin wakilin Aminiya ya yi tattaki zuwa ofishinsu da ke shiyyar domin samun karin bayani amma hakarsa ba ta cin ma ruwa ba saboda D.P.O. ba ya nan, kananan jami’an da ke ofishin kuma sun ce ba za su yi magana da dan jarida ba.