Dan shekara 71 ya dirka wa ’yar masu haya a gidansa ciki
Sakamakon gwajin ya nuna ba wannan ne karon farko ba, domin kuwa yarinyar na dauke da cikin makonni shida
An kama wani dan shekara 71 bisa zargin yin lalata da ’yar wani magidanci da ke haya a gidansa ’yar shekaru 14, har ta samu juna biyu.
An ce an kama tsohon wanda ma’aikacin asibitin ne yana lalata da yarinyar ’yar shekara 14 a cikin bandaki a a Karamar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun.
Yarinyar ta shiga bandakin gidan ne domin yin wanka, amma bayan ’yan mintoci sai mai gidan ya bi ta cikin bandakin inda ake zargin ya yi lalata da ita.
Wasu mazauna garin ne suka gan shi, lamarin da ya sa ’yan sanda daga hedikwatar yankin Ajuwon suka kama shi.
- Matsafa sun yanke mazakutar dan shekara 2 a Neja
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Kudurin Hana Bankuna Cirar 0.5%
Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar.
Ta ce, “An kama tsare mai gidan. Mahaifin yarinyar ya ce an kama shi yana lalata da ’yarsa mai shekaru 14 a bandakinsu da safe.
“An kai yarinyar Asibitin Tamara da ke Akute kuma sakamakon gwajin da likitocin suka gudanar ya nuna cewa ba wannan ne karon farko ba, domin kuwa yarinyar na dauke da cikin makonni shida.
“Nan ba da dadewa ba rundunar CID ta jihar za ta fara gudanar da bincike a kan lamarin,” in ji ta.