dan shekara 71 ya yi lalata da ‘yar bazawarar da zai aura

Asirin wani tsoho ya tonu a lokacin da aka kama shi ana zarginsa da laifin yin lalata da ‘yar da bazawararsa ta haifa.Wakilinmu ya yi kicibis da wannan tsohon lokacin da wadansu matasa suka kama shi suna ta bugunsa suna yi masa ihu bisa zargin kama shi da aka yi da wata yarinya ‘yar shekara […]

dan shekara 71 ya yi lalata da ‘yar bazawarar da zai aura
dan shekara 71 ya yi lalata da ‘yar bazawarar da zai aura

Asirin wani tsoho ya tonu a lokacin da aka kama shi ana zarginsa da laifin yin lalata da ‘yar da bazawararsa ta haifa.
Wakilinmu ya yi kicibis da wannan tsohon lokacin da wadansu matasa suka kama shi suna ta bugunsa suna yi masa ihu bisa zargin kama shi da aka yi da wata yarinya ‘yar shekara goma.
Shi dai wannan tsoho mai suna Mahammadu Lawal, wanda aka fi sani da suna Bagi, mai kimanin shekara 70 , ya na  zaune ne a  Hayin Ojo Sabon Garin Zariya da ke jahar Kaduna. Binciken Aminiya ya nuna cewa Mohammadu Bagi ya dade yana lalata da wannan yarinya.
Aminiya ta tattauna da jagoran matasan da suka kama Bagi mai suna Mustafa Yusuf, wanda ya bayyana cewa, “ni dai ina sana’ar sai da shayi ne a Hayin Ojo da ke Sabon Garin Zariya, kuma shagona da nake sana’ar sayar da shayi yana kallon dakin tsoho Bagi ne, don haka kullum sai in ga wannan yarinyar ta zo ta shiga, can bayan kamar awa daya sai in ga ta fito a guje. Ana cikin haka, sai ran nan na tsare ta na ce ‘’ke mai kike zuwa yi a nan?’’ sai ta kama kuka, ta ce mun ya ba ta N80, na kwace, na ce idan na kara ganinki kin zo nan  zan fada wa babanki. Duk da a lokacin ban san ko waye babanta ba.’’
“To kwana biyu sai na ga ta daina zuwa, ashe idan za ta zo tana zuwa ne kamar misalin karfe shida na safe, to sai a wannan karo ta sake lokaci ta zo bayan sallar magariba, wato misalin karfe bakwai da rabi na yamma, sai na ga ta shiga dakin suka ja kofa suka rufe, to ni kuma sai na kira mutane tare da Mai Unguwa domin su gani. Muna tsaye sai suka bude kofa, sai yarinyar ta fito, sai muka kama ta muka ce mata me ta zo yi? sai ta ce ya kira ta ne. Sai na ce mata “ba na hana ki zuwa nan ba?’’ Sai ta ce ei ka hana ni.’’’
Ya cigaba da cewa, ‘’daga nan sai muka dunguma zuwa gidan Sarki tare da shi wannan tsoho, inda aka tambaye shi abin da ya hada shi da yarinyar, sai ya ce wai yana aikenta ne, kafin daga baya ya amsa cewa yana lalata da ita ne. to ka ji yadda aka yi.’’
 Wani mai sarauta wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce yarinyar ‘yar uwarsu ce, domin uwar yarinya mai suna Furera matar dan uwansu ce, kuma ya rabu da ita ne, bayan rabuwa da ita ne sai ta tafi da yarinyan gidanta.
Wakilinmu ya gano cewa, shi wannan  tsohon Lawal Bagi zai auri mahaifiyarta ne, kuma har an shirya za su yi aure, amma saboda shi yana shirin aurar da daya daga ciki ‘ya’yansa shi ya sa suka daga auransu.
Da Aminiya ta tatttauna da tsohon ya bayyana mata cewa, “sunana Mohammadu Lawal, amma an fi sanina da Bagi, saboda sanar’ar sai da kayan miya da nake yi. Lallai ina lalata da wannan yarinya tun ba yau ba, amma ni a sanina ban yi lalata da ita da ya wuce sau uku ba, kuma ni ma abin da ya sa nake lalata da yara don ni ma ana yi da nawa ne.’
 Da Aminya ta nemi sanin ko yana fama da tabin hankali, sai tsoho Bagi ya ce, ‘’yaro babu abin da ya same ni, lafiyata lau kamr kowa, kuma ni asalina mutumin Malumfashi ne da ke Jahar Katsina, amma na shekara a kalla 30 a garin nan, kuma na auri mata da dama, domin na yi auri mata kamar 20, sai dai da mata daya na haihu, kuma ina da yara goma, mata 4, maza 6.’’
Da aka ko yanzu ya yi nadama? Sai ya ce, “ na yi nadama, kuma idan Allah Ya so ba zan kara ba.
Da Aminiya ta tunrubi yariyar sai ta ce, ‘’ni ban taba wannan harka ba, shi ya fara mun, domin ranar da ya fara da ni sai da ya ji mun ciwo har jini yana ta zuba a jikina, ko da na je na fada wa mahifiya ta sai ta ce in yi shiru kada in bari kowa ya sani, kuma ita ta kai ni wajen magani kuma ta rika gasa mun da ruwan zafi.’’
Aminiya ta yi kokarin saduwa da mahaifinyar yarinyar mai suna Furera, amma ta gudu ta bar garin saboda faruwar  wannan lamarin.
Sashin bincike na ‘yansanda da ke  Zariya ya tabbatar da faruwar lamarin, a inda jami’an ofishin suka ce sun tura su asibiti domin samun rahoton likita kafin su gane gaskiyar lamarin.