dan shekara 82 ya yi shekara 47 yana yin jarabawa bai ci ba

Shib Charan wani Ba’indiye dan shekarara 82 da ke Rajastan, ya shafe shekara 47 yana yin jarabawar sakandare, inda a kowace shekara yake kara faduwa. Mutumin dai ya yi alwashin yin aure ne kawai da zarar ya ci jarabawa.Sakamakon jarabawar sakandare da hukumar jarabawa ta Rajastan ta fito das hi a yammacin ranar Lahadi, ya […]

dan shekara 82 ya yi shekara 47 yana yin jarabawa bai ci ba
dan shekara 82 ya yi shekara 47 yana yin jarabawa bai ci ba

Shib Charan wani Ba’indiye dan shekarara 82 da ke Rajastan, ya shafe shekara 47 yana yin jarabawar sakandare, inda a kowace shekara yake kara faduwa. Mutumin dai ya yi alwashin yin aure ne kawai da zarar ya ci jarabawa.
Sakamakon jarabawar sakandare da hukumar jarabawa ta Rajastan ta fito das hi a yammacin ranar Lahadi, ya kara kawo wa auren wannan mutum tarnaki, domin ya fadi. Mutumin wanda aka saba yi wa lakabi da Sheojiram da Pappu, mazaunin kauyen Kohari ne da ke garin Behror, kimanin kilomita 140 daga inda yake daukar wannan jarabawar.
A lokacin da yake ganiyar samartakarsa, ya yi alwashin yin aure ne kawai da zarar ya ci jarabawa.
“Har zuwa wanan lokaci da nike raye, zan ci gaba da yin jarabawar,” inji Shib Charan, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na IANS, ranar Litinin da ta gabata.
Shib charan, wanda a halin yanzu yake zaune a dakin ibadrar Indiyawa, yana rayuwa d akudin fensho da gwamnati ke biyansa.
“Baya ga cin jarabawa, zan ma samu damar yin aure,” inji shi.
Saboda nisan shekaru, yana fama da matsalar ciwon ido da kunne, har ma da tafiya, amma duk da haka burin sa ya ci jarabawa. “A shekarar 1995 na ci mafi yawan darussan da na zauna, ban da lissafi,” a cewarsa.
Wani abin takaicin a wannan karon bai ci kowane darasi ba. A wasu darussan ma sifili ya ci.
Shib Charan ya fara rubuta wannan jarabawar ne tun a shekarar 1969. Kuma tun daga wancan lokacin cin jarabawar ya zame masa karfen kafa.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano