dan shekara 93 na motsa jiki da gwajin kwanji

dan shekara 93 yana gwajin kwanji da motsa jiki fiye da sauran matasa, ala’amarin da ya danganta da kasancewarsa ya shafe shekara 20 yana motsa jiki. A cewarsa, a kalla ya rika shafe sa’a guda a kullum wurin wasannin motsa jiki, don rage karsashin tsufa a jikinsa. Wannan tsoho dan shekara 93, mai suna Shen […]

dan shekara 93 na motsa jiki da gwajin kwanji
dan shekara 93 na motsa jiki da gwajin kwanji

dan shekara 93 yana gwajin kwanji da motsa jiki fiye da sauran matasa, ala’amarin da ya danganta da kasancewarsa ya shafe shekara 20 yana motsa jiki. A cewarsa, a kalla ya rika shafe sa’a guda a kullum wurin wasannin motsa jiki, don rage karsashin tsufa a jikinsa.

Wannan tsoho dan shekara 93, mai suna Shen Hua, ana yi masa lakabi da “Kaka mai kwanji’ ko “Muscular grandpa,” yadda masu mu’amala a shafukan sadarwa na intanet a kasar Sin ke kiransa. A duk lokacin da Shen Hua ya ziyarci wurin wasan motsa jiki na gundumar Liwan da ke birnin Guangzhou, sai matasa su yi ta gaishe shi, har ma wasu na nuna son ganawa da shi. A wasu lokutan har baki ’yan kasar waje kan roke shi, a yi musu hotuna tare.
Shen Hua dai ya saba yi wa wannan gidan motsa jiki ciniki. Kuma a kusan kowane karfe uku na rana yakan je wannan gidan motsa jiki, don motsa jikinsa.
Wani mai horar da mutane dabarun motsa jiki tsawon shekara 10, ya ce ya dade bai ga mutanen da tsufansu ya wuce shekara 70 suna yin irin gwajin kwanjin TRd da wannan tsoho dan shekara 93 ke yi.,
Kuzarin wannan tsoho ya sanya an tabbatar da cewa, mutum komai tsufansa bai makara ba, tunda Shen Hua kafin ya ajiye aikinsa ya yi aiki tukuru, har ta kai ga ba shi da lokacin motsa jikinsa. Shen Hua ya fara dabarun motsa jiki ne bayan da ya kai sheekara 70 .
Labarin wannan tsoho dan shekara 93 ya bazu a shafukan sadarwar intanet da ake hulda da su a kasar Sin.