dan shekara biyu mai shan karan sigari 40 a rana ya koma cin abinci da ya kai shekara biyar

Labarin da jaridar Aminiya ta buga na yaro dan shekara biyu da ke shan karan sigari 40 a rana, da ya fita a ranar Juma’a 4 ga Yuni, 2010 yanzu al’amarin ya canza salo bayan da yaron ya kai shekara biyar.Rahoton ya tabbatar yanzu yaron mai suna Aldi Rizal ya koma dirkar abinci ne babu […]

dan shekara biyu mai shan karan sigari 40 a rana ya koma cin abinci da ya kai shekara biyar

Wani yaro yana cin abinci (tsohuwar ajiya)

Dan shekara biyu Aldi Rizal yana busa sigariGwani na Gwanaye: Anan yana busa hayaki sama ne

Labarin da jaridar Aminiya ta buga na yaro dan shekara biyu da ke shan karan sigari 40 a rana, da ya fita a ranar Juma’a 4 ga Yuni, 2010 yanzu al’amarin ya canza salo bayan da yaron ya kai shekara biyar.
Rahoton ya tabbatar yanzu yaron mai suna Aldi Rizal ya koma dirkar abinci ne babu kakkautawa a duk bayan kankanen lokaci maimakon zukar taba sigari da mahaifiyarsa ta yi kokarin hana shi yin hulda da ita.
Rahoton da kafar sadarwar naij.com ta kalato ya nuna, yaron tun yana dan shekara biyu ya fara yin harka da sigari al’amarin da ya sa yanzu haka ya zama kwararren kabusa.
Sai dai ya zuwa yanzu, mahaifiyar yaron ta ce ya fara sassautowa a kan harka da sigari ya koma lodar abinci da ya ke yi.
Mahaifiyar ta ce yakan dauki lokaci mai tsawo yana dibar girki, girkin da ko  babban mutum da kyar zai iya cinye shi.
An gano Aldi Rizal ne a wani kauye mai suna Sumtra da ke kasar Indonesiya a lokacin da yake busa sigari tun yana dan shekara biyu a lokacin da yake tuka kekensa al’amarin da ya ba jama’a da dama mamaki.
Sai dai kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa yanzu haka ana kokarin hana yaron yin hulda da sigari wajen hana shi ganinta balle ya yi tunanin zukarta.  Sai dai mahaifiyar yaron ta ce ya zuwa yanzu dan nata yakan dame ta da kuka don ta sayo masa kwalin sigari amma sai ta yi kememe don kokarin ganin ta hana shi yin hulda da sigari musamman wajen ceto rayuwarsa daga fadawa cikin hadarin da ke tattare da shan ta.
Mahaifiyar yaron ta ce ta lura tun lokacin da ta cire danta daga taba sigari kafafuwansa suka kumbura kuma suka tsattsage al’amarin da yanzu haka yake tayar mata da hankali.
 Nan kuma Aldi Rizal ne yake dibar girki bayan an hana shi yin hulda da sigariTa ce a halin yanzu hankalin danta ya fi karkata ne wajen lodar abinci a duk bayan kankanen lokaci tun bayan da ya daina shan sigari.
“Farko a lokacin da Aldi ya bar hulda da sigari, ya koma yin wasa da ’yar tsana ce amma kuma daga baya sai hankalinsa ya karkata wajen cin abinci babu kakkautawa”, inji mahaifiyarsa.
“Yakan buga kansa a bango a duk lokacin da ya nemi wani abu na hana shi, kuma yin haka ne ta sa tun farko na kyale shi wajen yin hulda da sigari musamman ganin zai iya cutar da kansa ta hana buga kansa a bango ko dutse ko kujera ko duk wani abu da ke kusa da shi don yaro ne mai zuciya kuma abin yakan tayar mini da hankali a duk lokacin da yake haka”, inji ta.s
Yakan shafe lokaci mai tsawo yana rusa ihu idan bai samu abin da yake so ba don haka nake haba-haba da shi a mafi yawan lokuta.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan