dan shekara takwas ya zama mai wa’azin kasa a Dubai

Wani yaro dan shekara takwas, Ba’indiye ya zama mai wa’azin kasa a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). Yaron, mai suna Ibrahim Fahim Shabandri, ya shiga gasar Larabci da wa’azin Musulunci a tsakanin kananan yara 70. Ibrahim Fahim Shabandri, ya gwada kwarewa a magana da harshen Larabci, kamar yadda jaridar Khaleeejtims ta ruwaito.Shi kuwa […]

dan shekara takwas ya zama mai wa’azin kasa a Dubai
dan shekara takwas ya zama mai wa’azin kasa a Dubai

Wani yaro dan shekara takwas, Ba’indiye ya zama mai wa’azin kasa a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). Yaron, mai suna Ibrahim Fahim Shabandri, ya shiga gasar Larabci da wa’azin Musulunci a tsakanin kananan yara 70. Ibrahim Fahim Shabandri, ya gwada kwarewa a magana da harshen Larabci, kamar yadda jaridar Khaleeejtims ta ruwaito.
Shi kuwa mahaifin yaron, wato Faheem Ahmed, ya bayyana cewa, wannan kyauta za ta kara wa dansa kwarin gwiwa wajen koyom harshen Larabci. Ibrahim dama dalibi ne a makaranar haddar Alkur’ani da ke Ibn Khaldooni a Dubai da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
“Wannan abin farin ciki ne ga zuri’armu. Nasarar da ya samu sakamako ne na kwazo da aiki tukuru, don haka muna alfahari da ita,” inji mahaifinsa.
Wannan gasa ta yara masu wa’azi, ita ce karo na 13 da Sashen kula da Yawon shaktawa da Harkokin Tallatata ta shirya, karkashin jagorancin, Shaikh Ahmed bin Mohammed bin Rashid Al Maktoum, shugaban Mu’asassar (Cibiyar) Mohammed Bin Rashid Al Maktoum.
Alkalan da ya tantance masu gasar, Sheikh Omar Saad, wanda babban mai wa’azi ne a sashen harkokin adinin Musulunci da ayyukan jinkai; sai Bader Jumaa, Farfesan Larabci a Makarantar Omar Bin Al-Khattab Model School da Lewis Bullock, daya daga cikin jami’an Cibiyar Al’adu ta Dubai. An dai zavi yara 12, wadanda suka fafata a karshen gasar, a fannonin da suka hada da huduba da waken adabin Larabci.
Shugaban Cibiyar da ta shirya gasar, Muhammad AlHashemi, ya ce, ana shirya gasar ne don zakulo masu hazaka, wadanda suka kware a huduba da waken adabin Larabci. Kuma wadanda suka cancanci shiga gasar, yara ne da shekarunsu suka kama daga shida zuwa 11.